Shugabanin adawa a Togo sun ce, ba abin da su ke bukata face sauya kundin tsarin mulkin kasar, sabanin sauye sauyen da gwamnati ta yi alkawarin samarwa. Hakan dai na zuwa ne bayan zanga zangar kin jinin gwamnatin da ‘yan adawar suka rika gudanarwa a baya-bayan nan, wadda ta samu halartar dubban ’yan adawa a manyan biranen kasar.
Eric Dupuy, kakakin hadakar jamíyyun adawar 5 Cap 2015 – kungiyar da ta jagoranci zanga-zangar ranakun Laraba da Alhamis, domin ganin a siyasance an samar da sauyin gwamnati a Togo, ya danganta sauye sauyen da gwamnatin ta ce za ta samar a matsayin jan kafa, inda ya ce ba shi ne abin da su ke bukata ba.
Shugaban kasar ta Togo, Faure Gnassingbé, ya dare kan karagar shugabancin kasar shekaru 12 da suka gabata bayan mutuwar mahaifinsa, Gnassingbé Eyadéma.
Mahaifinsa janar Eyadéma ya mulki ’yar karamar kasar ta Togo da ke yankin Yammacin nahiyar Afrika na tsawon shekaru 40 sakamakon wani juyin mulkin soja da ya yi wa gwamnatin farar hula.
Yau shekaru 10 ke nan ’yan adawar ta Togo ke bukatar ganin an sake fasalta kundin tsarin mulkin 2002 da aka kwaskwarimance, musaman ta bagaren sake mai do da dokar takaita wa’ádin shugabancin kasa shekaru 10 a wa’ádin shekaru biyar-biyar sau 2 babu kari.
A wata sanarwar bayan taron majalisar ministoci ta marecen ranar Talatar da ta gabata, gwamnati ta yi wani yinkuri da ake ganin sassauci ne akan matsayinta, inda ta bayyana aniyar samar da gyare gyare ga kundin tsarin mulkin musaman ta bangaren takaita wa’ádin shugabanci da kuma tsarin zabe da ke kunshe a kundin.