Idris Aliyu Daudawa" />

Tsarin Rundunar Sama A Kan Bunkasa Tsaron Cikin Gida

NAF

Fiye da shekara goma ke nan yadda kasar Nijeriya ta samu kanta cikin wani al’amari na fara yin arrangama da ‘yan ta’adda ko kuma wadanda ke tada tsaune tsaye, ko kuma ‘yan kungiyar Boko Haram, wadanda sojoji a aikin su wanda suka saba yin shi dama na ka kare kasa wanda tsarin mulki ne na kasa ya dora a kansu, inda suke ta arrangama da su ‘yan ta’adda duk domin su kare kasa. Amma kuma wani abu mai daure kai shine abu ne wanda ya fara kamar wata ‘yar zanga- zanga ko kuma tayar da zaune tsaye sai ga shi ya koma al’amarin da ake kira yaki da su ‘yan ta’ddar. Ya zuwa wanin lokaci dai sai wannan yakin da ake yi ya kuma dauki wani sabon salon saboda kuwa ya kasance dole ne sai a n yi tunanai na bullowa da wasu sababbin hanyoyi na yadda za’a tunkari shi yakin, saboda a kawo karshen shi. Duk da yake rundunar mayakan sama sun kame duk wuraren da su ‘yan ta’addar suke yanzu sojoiji sun amso su, amma har yanzu da akwai bukatar a sake, yin wasu tsare- tsaren, sanin kowa ne rudunar sojojin sama wata hanya ce daya wadda aka takama da ita, wadda kuma za’a iya shigar ma su ‘yan ta’addar, da yake akwai maganar amfani da jiragen saman yaki ta sama na zamani, wadanda su ‘yan ta’ddar ke amfani dasu wajen kai hare- hare. Saboda a samu kawo ma kokarin da su’yan ta’addar suke yi sai ita rundunar sojojin sama ta yaye wani sahu na sojojin yaki na musamman, ranar 15 ga watan Maris na wannan shekarar saboda a kata taimaka ma bangarorin ayyukan nasu.
Darektan hulda da jama’a da kuma sadarwa na rundunar Air Coimmander Ibukunle Daramola ya bayyana cewar su dakarun wadanda aka yaye na musamman 17 ne, wadanda kuma suka samu nasarar kammala kwas na 4 na shekarar 2019. Shi dai kwas (horarwar) ta mako goma ne na horarwar sosai, wanda suka yi a Kaduna.
Ya ci gaba da bayanin cewar shi wannan al’amarin na haorar da sojojin yaki ta sama na musamman wannan shine lokaci na farko da aka horar da kuma yaye sosoji na musamman, wanda kuma ita rundunar sojojin sama ce ta dauki nauyin al’amarin haorar da su, wannan shine manufar shi Babban hafsan sojojin sama, wanda yuake son ayi amfani da al’amarin dogaro da kai, sai kuma lura da sa idanu akan yadda ake kashe kudaden rundunar sojojin sama.
Ya ci gaba da bayanin cewar kafin dai akai ga zuwa wannan lokaci rundunar tana yin amfani ni ne da wani kamfani na kasar Isra’ila, wanda wata tawaga ce ta mutane 4, wadanda sune suka harar da rundunar mayakana nan musamman, wannan kuma ya hada ne da wasu kwas- kwas din da ake yi a kasashen waje, irin su Belarus, China, da kuma Pakistan.
A cikin na shi jawabin lokacin da ake yin bikin yaye dalibai Abubakar ya bayyana cewar, a cikin shekaru hudu wadanda suka wuce, ita rundunar sojojin sama ta yi kokarin gyaran fuska ga ita rundunar saboda kawo gyara ga ita rundunar sojojin sama.
Shugaban rundunar sojojin saman ya bayyana cewar domin a ci gaba da yin al’amura kamar yadda ya kamata, wannan abin ya shafi horar da su jami’an, saboda a kara masu karsashi wajen yin aikin nasu.
Abubakar wanda ya nuna farin cikin shi saboda yadda aka gabatar da ita horarwar, sai ku8mam irin gudunmawar da su sojojin ko kuma mayakan na musamman, ganin irin gudunmawar da suke bayarwa wajen yaki da kungiyar Boko Haram da kuma sauran ‘yan tayar da kayar baya.
Ya ci gaba da bayanin cewar nasarorin da ita rundunar sojojin samak ta samu sun hada da, ‘yan ta’addar da ba’a dade da kamawa baa Birnin Gwari cikin jihar Kaduna, tare kuma da kuma yadda su jami’an sojojin sama wadanda aka kai saboda su taimaka bwa ‘yansanda lokacin da aka yi zabubbukan da suka gabata, wannan kuma aan yi la’akari ne da yadda suka gabatar da ayyukan su cikin nuna kwarewarsu. Kamar yadda ya kara bayani duk wannan yana nun aba da gangan rundunar take ba, wajen al’amariu na samar da wata tawaga ta musamman.
Shugaban rudunar sojojin saman ya yi kira da wadanda aka yaye cewar su yi kokari wajen, amafani da kwarewar da kuma horon da suka samu, a duk wasu ayyukan da za’a tura su nan gaba, su yiu amfani da juriya, hakuri, da kuma aaiki tukuruaiki tukuru, duk kuwa da yake ya yi kira da su rundunar ta musamman, da su rika gabatar da kansu kamar yadda dokokin ita rundunar sojan sama suka shimfida. Kamar gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da ayyukan su.
Ya jinjina ma Air Officer ko kuma babban jami’in horarwa na rundunar sojojin sama Air Bice Marshall Idi Amin, har ma da sauran wadanda suka taimaka ma shi, wajen saken fuskar yadda rundunar sojoji ta sama take.
Hakanan ma ya gode babban Shugaban askarawan Nijeriya kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari, saboda yadda yake bada kulawa ta musamman ga duk bukatun rundunar sojojin sama. Ya ci gaba da bayanin cewar “Kulawar da gwamnatin tarayya take bamu, ko shakka babu ya bayar da taimakawa wajen du wani ci gaban da rundunar ta samu, koma wanne iri ne. Hakanan ma ya nuna jin dadin su akan irin gudunmawar da jami’an rundunar suak bayar maza da kuma mata.
Ya kara jaddada cewar shi gaban da ita rundunar sojoji ta sama take samu,wannan ya nuna cewar taimakon da gwamnatin tarayya take basu ba maganar wasn yara bace.
Ya ci gaba da bayanin cewar su patchers wadanda aka kawo su daga wasu wurare saboda a samu karin kulawa da tsaron cikin gida, duda goma sha hudu ne, an kuma kais u jahohi goma sha hudu, za kuma su taimaka ne wajen samar da tsaro.
Shi ma a nashi jawabin kwamandan BTC Wing Commander Stephen Sekegor ya bayyana dalilan da suka sa aka mayar da shi al’amarin horar da runduna ta musamman ta sojan sama a gida, an yi hakan ne saboda a tabbatar da ana kashe kudaden rundunar kamar yadda doka ta shimfida da kuma horarwa mai nagarta.
Ya kuma gode ma shi Shugaban rundunar sojojin sama na Nijeriya aka abinda ya kira tsari shi na Shugabanci nagari da kuma bayar da shawarwarin da suka kamata.
A wani ci gaba kuma rundunar sojan sama ta kasa ta horar da jami’ai 360 wadanda suma za su taimaka ne wajen samar da tsaro na musamman. Shugaban rundunar ta sama ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi, daidai lokacin da ake yi taron kara ma juna sani na al’amarin daya shafi tsaro ta shekarar 2019 wadda take da taken ‘’Yadda za ‘a taimaka wajen samar da tsaron wuraren ayyukan rundunar sojoji ta sama saboda kare su.

Exit mobile version