Tsarin Shugabancin Hausa/Fulani Gabanin Zuwan Bature

Hausa/Fulani

Kamar yadda muka yi bayani a makon jiya, a tsarin zamantakewar Hausawa, kowane gari yana da shugaba wanda duk sa ran jama’ar da ke zaune a garin suna bin umarnisa ne. Tsarin shugabanci na Hausawa yana tafiya tun daga kan mai unguwa wanda shi ne yake da ikon jagorantar dukkanin al’amuran da suka shafi unguwarsa. Kuma shi ne ke yi wa jama’arsa Jagoranci a kan kowane abu da ya shafi unguwarsa. Yana kula da al’amurasu na yau da kullum ta fuskar zama a matakin unguwanni.

Mai-Gari: shi ne ke yi wa jama’arsa Jagoranci a kan kowane abu da ya shafi rayuwa. Duk wata husuma da ta shi tsakanin mutanen gari. Shugabancin mai-gari yana da matukar karfin gaske, don kuwa ya kan iya korar mutum daga yankin kasarsa.

Ire-iran nauyin da ya rataya akan sha’anin Jagoranci Mai-gari, ya hada da sulhu ta yadda za’a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da jin dadi.

Ba’a nan salon mulkin ya tsaya ba tun da mai-gari ya na karkashin ikon dagaci, shi kuma dagaci a karkashin ikon Hakimi ya ke, wadda Hakimi shi ne shugaban gari ko lardi kasa wanda duk garuruwan da ke karkashin ikon dagatai su ke karkashinsa.

Dagaci

Dagaci ne yake nada mai unguwa, amma bisa aminciwar Hakimi, daga biya sai shi dagaci ya dawo ga al’ummarsa wajen zabar wanda ya fi da cewa ya zama Dagaci. Haduwar unguwanin da yawa a waje guda shi ya samar da gari, Dagaci ne yake jagoranta al’ummar wannan garin.

Dagaci shi ne idon hukuma a garinsa. A duk lokacin da hukuma take son yin hulda da jama’ar garin baki daya, to ta hannunsa ake bi, shi kuma sai ya isar da sakon ga masu unguwanninsa, ta hanyar bijiro musu da bukatarsa ko kuma fatansa a kan wani sha’ani.

Hakimi:

Hakimi shi ne shugaba da yake kula da garuruwan da ke cikin yankin kasarsa. A matsayinsa na shugaban lardi da ma kuma gunduma. Shi ne mai yin shari’a ne da sasanta jama’a wato yin sulhu tsakanin jama’arsa idan wata rigima ta tashi wadda ta shafi talakawansa, to a nan zai bugi kirji ya yi ruwa da tsaki wajen sasanta al’amarin da kuma hukunta duk wanda a ka samu da aikata laifi. Sannan kuma shi ne mai bayar da umarni dangane da wasu abubuwa da ka iya tashi na gaggawa don al’umma su fadaka, ko kuma sha’ani na tsaro ko kuma wayar musu da kai akan cigaba da a ka samu. Zai umarci Dagatai da masu unguwanin da su sanar da jama’ar su wani sako da ya ke bukata su sani.

Wannan kujera ta Hakimi kuwa ba a gadonta. Sarki ne yake nada wanda ya so daga cikin ‘ya’yansa da kuma makusantansa, shi Hakimi yana  wakiltar sarki ne.

Bari mu dan wai waya baya, domin mu kalli mulkin gargajiya ta fuskar tarihi a inda Hausa/Fulani suka samu tsari da kuma yanayin gudanar ta Jagoranci.

Bayan Jihadi na Shehu Usmanu Dan Fodio (1804-1810), yunkurinsa na kafa Daular Musulunci da kuma tabbatar cewa al’umma sun hau gwadaben shari’ar Isilama.  A wannan lokacin ya samu damar wanzar da ikonsa na ganin kowa ya amsa kira ga abin da ya zo da shi. Wanda ya hada jihohi 14 yankin Arewa.

Hakika wannan dama ce da Mujaddadi ya samu na iya kasa tsarin mulkin zuwa gida biyu, inda sakkwato da Gwandu su ke da tsarin Jagoranci masauratu.

La’akari da rabe-raban tsarin mulkin a wan can lokaci, ko kuma taswira da kuma salo, ya janyo kakkasuwar ragamar gudanar da shugabanci a mataki daban-daban. Shi ne ya bai wa sarki damar zama mai fada aji har da ma cikakken iko ko kuma dama.

Wannan tsari shi ne ake bi tun kafin zuwan musulunci da turawan Yamma.

Exit mobile version