Tsaro: Akwai Bukatar Gwamnati Ta Mike Tsaye A Nasarawa – Adamu Doya 50

Jigo a siyasan APC a jihar Nasarawa kuma Babban manomi jagoran talakawa, Malam Adamu Usman Doya 50, ya yi kira ga Gwamnati da ta dubi Allah ta dubi Talakawa ta gaggauta samar  tsaro a hanyar Akwanga zuwa Lafia.

Ya ce; yanzu abin da ake kukansa sai kara yawa yake yi saboda matsalar tsaro yau har Mataimakin Gwamnan ake kaiwa hari.

Malam Adamu Usman Doya 50 ya ce; Mukaddashin Gwamnan ya taho da motar Gwamnati amma aka tare shi aka kashe Jami’an tsaron sa to ina kuma ga talakawa?.

Ya ce; Gwamnati ta mike tsaye duk Wanda aka samu da laifi komin girmansa ko da waye ko a cikin Jami’an tsaro ne a hukunta shi saboda ya zama darasi ga na gaba.

Ya ce, tun da Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya hau kan mulki a shekarar 2015 ya fara fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram, kuma ana samun sauki sosai a wannan lokacin.

Amma saboda rashin kishi na wasu mutanen da ba su bukatar ci gaban kasa suka bullo ta wani hanya yanzu sun ruguza harkan tsaro gabaki-daya.

Wani abin takaici a kan samu sa hannun wasu Jami’an tsaro cikin aikin Ta’addanci. Wannan munafintar Gwamnati ne.

Ya ce; a cikin ‘yan siyasa akwai wadanda ba su bukatar su ga wannan Gwamnatin ta Buhari ta yi abin arziki duk da cewa su ne suke rike da manyan mukamai na Gwamnati ko a bangaren tsaro.

Sannan ya yi kira ga Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, da ya dage da ayyukan alheri na ci gaba da yake yi domin raya jihar Nasarawa.

Ya ce ; Gwamnan ya dauki duk matakin da ya dace kuma kamar yadda ya bayyana cewa zai kara samo tallafin Jami’an tsaro daga tarayya to ya dage ka da ya yi kasa a gwiwa domin kare martabar al’umman jihar Nasarawa.

Exit mobile version