Tsaro Ba Aikin Hukuma Ne Kadai Ba -Sanata Yahaya 

ahaya Abubakar Abdullahi

Daga Jamil Gulma Birnin Kebbi

 

Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi shugaban masu rinjaye  a majalisar dattawa ya yi kira ga kira al’umma da su su bayarda nasu gudummawa wajen dabbaka abinda ya shafi tsaro a garuruwan su day wajen ayukansu.

Ya yi wannan bayani ne jiya da ya ke zantawa da manema labarai a gidansa da ke garin Argungu jim kadan bayan saukowa daga hawan Sallah.

Shugaban masu jinjaye Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi ya ce nuna jin tsoro da al’umma ke yi yana daga cikin abubuwan da ke karfafa wa wadannan miyagun mutane gwiwa. A duk lokacin da suka shigo gari ya kamata mutane su ma su tinkare su saboda ai su ma suna da rayuwa Kuma suna son rayuwar su saboda haka a duk lokacin da suka gano idan sun kai hari ana tinkarar su babu shakka za a sami sa’ida.

Ya kara da cewa  bayan wannan kowa yana da rawar da zai iya takawa wajen inganta tsaro saboda akwai hanyar sheda wa dagatai, hakimawa, Iyayen kasa har zuwa sarakuna da kuma jami’an tsaro a duk lokacin da suka ga wani mutum da ba su aminta da shi ba.

Haka zalika ya yi kira ga al’umma da su rungumi harkar noma da gaskiya wanda daman shi ne aka san kasar nan da shi musamman wannan yankin na arewa saboda yanzu haka akwai shirye-shirye na harkokin noma da kiwo da Kuma sana’o’i dabam-daban da gwamnatin tarayya ke yi saboda inganta rayuwar yankasa.

Exit mobile version