Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja
Sabon Babbam Sakataren ma’aikatar tsaro (MOD), Musa Istifanus, ya jaddada bukatar hadin kai a tsakanin dukkan jami’an tsaro domin kawo karshen matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar Sojin saman kasa nan (DOPRI), Air Commodore Edward Gabkwet, ya fitar kuma yaba wa manema labarai a Abuja, inda yake cewa, Sakataren ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai zuwa hedikwatar rundunar sojojin saman Nijeriya (Hk NAF), Abuja.
Babban Sakataren, wanda ya samu rakiyar daraktoci daga ma’aikatar na MOD, ya samu tarba daga Shugaban hafsan sojojin sama (CAS), Air Marshal Oladayo Amao, Shugabannin reshe da sauran manyan hafsoshi. A yayin da yake taya Shugaban sojin sama murna kan karin girmar da ya samu a baya da kuma sabon matsayin da ya samu na Air Marshal, Istifanus ya bayyana cewa, ya kasance a hedkwatar NAF ne domin ya fahimci ayyukan NAF da kuma kalubale don bawa ma’aikatar damar samun bayanai kamar yadda ya dace.
Da yake ci gaba da magana, Babban Sakataren ya bayyana cewa, ma’aikatarsa za ta ci gaba da tallafawa NAF a yakin da take yi da tayar da kayar baya da sauran nau’ikan aikata laifuka a kasar. A cewarsa, yakin da ake yi da tayar da kayar baya, yaki ne na bai daya da wakilan sharri. Don haka ya yi kira ga Ma’aikatan da su yi aiki cikin hadin kai da kuma kara himma domin samar da zaman lafiya a kasar da kuma ba wa ‘yan Nijeriya damar ci gaba da kasuwancinsu na yau da kullum. Ya kuma nuna kwarin gwiwarsa na cewa akwai yiwuwar kawo karshen yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya muddin dai jami’an tsaro za su yi aiki tare tare da hada kai da juna.
Istifanus ya kuma yi amfani da lokacin ziyarar tasa don yin ta’aziyya ga shugaban a kan rashin da aka yi na mutuwar jami’an NAF guda 7 wacanda kwanan nan suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama.
A jawabinsa, Shugaban ya taya Istifanus murnar zama Babban sakatare kuma ya nuna jin dadinsa kan goyon bayan da yake baiwa NAF. Ya kuma bayyana cewa, nasarorin da sojojin Nijeriya suka samu a baya-bayan nan a kan masu tayar da kayar baya da kuma ‘yan bindiga, an danganta shi da babban hadin kai tsakanin dukkan jami’an tsaro.
Ya kara da cewa, za su ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba har sai kasar nan ta kawar da dukkan nau’ikan aikata laifuka. Daga nan Air Marshal Amao ya roki Babban sakatare da tawagarsa na Daraktoci don taimaka wa NAF don ba ta damar cimma nasarar da kundin tsarin mulki ya ba ta. Ya kuma yaba wa kokarin da Ma’aikatar ke yi na sayo wasu dandamali na hukumar, yayin da ya kuma bayyana cewa, NAF ta fara karbar kayayyakin wasu jiragen sama da ta saya tun farko.
Wani muhimmin abin ziyarar shi ne, shimfidar furannin da Babban Sakatare ya yi a hedkwatar NAF din, domin girmamawa ga jami’an NAF din da suka rasa rayukan su a yayin da suke bakin aiki.