Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari zai fede biri a bainar jama’a kan tabarbarewar harkokin tsaro da ke addabar kasar, musamman ma Arewacin Nijeriya ranar Alhamis mai zuwa lokacin da zai bayyana a gaban Majalisar Wakilai Kasa.
Majiyar Fadar Shugaban Kasa ta shaida wa LEADERSHIP A YAU cewa, hakan ya biyo bayan amincewar da Shugaba Buhari ya yi ne na gabata a gaban majalisar sakamakon gayyatar da su ka yi ma sa bayan da a ka kai mummunan harin kisan kiyashin Zabarmari a Karamar Hukumar Jere da ke Jihar Borno, inda a ka kashe wasu manoma da masunta guda 43.
Majiyar ta ce, shugaban zai mayar da hankali ne kan harkokin tsaro dungurum a fadin kasar bakidaya, musamman ma Arewa.
Idan dai za a iya tunawa, a makon jiya ne Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Rt. Hon. Femi Gbajiamila, ya kai sakon kiranyen ’yan majalisar wakilan ga Shugaba Buhari, inda kuma bayan fitowarsa daga ganawar tasu ya shaida wa manema labarai cewa, shugaban ya amince da kiran da su ka yi ma sa, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba su iko.
Kisan kiyashin ya haifar da kiraye-kirayen neman sauke shugabannin tsaron kasar da ma shi kansa Shugaba Buhari. Ita kanta Majalisar Dattawan Nijeriya ta maimaita kiranta ga Shugaban Kasar da ya sauke shugabannin tsaron a karo na uku.
Ita kuwa Majalisar Wakilai ta nemi Shugaban Kasar ya gurfana a gabanta ne bayan wata tattaunawa mai zafi a tsakanin mambobinta, inda daga bisani a ka amince da kudirin kiran shugaban kasar bayan shugabannin majalisar sun yi ganawar sirri, don saisaita al’amura.
Jim kadan bayan amincewa da a kira Shugaba Buharin, don yin bayani kan tabarbarewar al’amuran tsarin ne, sai Kakakin Majalisar ya bazama Fadar Shugaban Kasa, don mika goron gayyatar.
Jim kadan bayan fitowarsa ne ya shaida wa mafarauta labaran fadar cewa, “mun amince da ranar da zai bayyana gaban majalisa, don yi ma ta bayanin halin da a ke ciki. Mun tsayar da rana, amma za mu sanar da ku nan gaba kadan,” in ji shi.
Sai a yanzu ne wata majiyar Fadar Shugaban kasar ta shaida wa LEADERSHIP A YAU cewa, an tsayar da ranar Alhamis mai zuwa, 10 ga Nuwamba, 2020, a matsayin ranar da Shugaban Kasar zai gabata a gaban majalisar.
Shi kuwa Malam Garba Shehu, mai magana da yawu Shugaba Buhari, ya shaida cewa, Shugaban Kasar zai yi jawabi ne ga majalisun dokokin kasar guda biyu, ba wai Majalisar Wakilai kadai ba, wato har da Majalisar Dattawa kenan.