Khalid Idris Doya" />

Tsaro: Darakta Janar Na NYSC Ya shawarci Masu Bautar Kasa

NYSC

Babban Darakta Janaral na hukumar ‘yan yi wa kasa hidima wato (NYSC), Birgediya Janaral Suleiman Kazaure, ya shawarci mambobin hukumar da suke ke muhimmatanta hidimar tsaro a kowani lokaci domin kariyan kai.

Shawarar tasa, na kunshe ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru wacce Daraktan yada labarai na hukumar ta NYSC Mrs Adenike Adeyemi, ta sanya wa hanu gami da raba wa ‘yan jarida, ta bayyana cewar shawarar ta zo ne a ranar Juma’a sa’ilin da ke shi DG din ke gabatar da jawabi wa mambobin NYSC rukunin ‘A’ a sansanin ‘yan yi wa kasa hidima da ke Obubra a jihar Kuros Ribas.

Ya kuma bukace su da a kowani yanayin da aka turasu suke kokarin nuna halin kwarai da kuma kyawawan dabi’u a cikin al’ummomin da aka turasu domin dacewa da asalin abun da ake son su riska a rayuwarsu na bauta wa kasa na tsawon shekara guda.

Ya kuma gargadi dukkanin mata da suke hidimar bauta wa kasa a wannan lokacin da suke kauce wa yin shigar banza da kuma sanya tufafin da ke dame musu jiki don kauce wa janyo hankulan mazaje kusa da su, gami da suke yin shiga daidai da al’adarsu da kuma al’akari da irin al’ummomin da suke rayuwa a cikinsu a hidimarsu ta bautar kasa.

Darakta Janaral na hukumar ta NYSC, Sulaiman Kazaure ya kuma bukaci masu hidimar bauta wa kasar nan, da suke bayar da dukkanin himmar da ta dace a wuraren da aka turasu domin kara daukaka darajar yankunan da kuma wuraren don gina kasar nan.

Babban jami’in shirin yi wa kasa hidima ta jihar ta Koros Ribas, Ambekemo Eniola, Ta shaida wa Darakta Janaral din cewar ‘yan yi wa kasa hidima su 2,116 ne suke samu horo a wannan sansanin a wannan lokacin na rukunin ‘A’.

Ta kuma shaida cewar kawo yanzu komai na ci gaba da gudunawa cikin kwanciyar hankali a wannan sansanin, tana mai cewa za kuma su ci gaba da sanya lura da hankali wajen gudanar da horon a wannan lokacin da sauran lokuta.

 

Exit mobile version