Tsaro: Gwamnan Neja Ya Nemi Al’umma Su Kara Sanya Idanu A Yankunansu

Yankunansu

Daga Muhammad Awwal Umar,

Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello yayi kira ga al’ummar musulmi da su zauna lafiya yayin gudanar da bukukuwan sallar Edul-fitr bayan kammala azumin watan Ramadan.
Gwamnan yayi kiran ne bayan kammala sallar Edul-fitr a babban masallacin Idin Kontagora.
Gwamnan ya taya al’ummar musulmi kammala azumin watan Ramadan da ya gabata, gwamnan ya janyo hankalin jama’a da su sanya idanu a mazaunansu kuma su sanar da duk wani labarin abinda ba su fahimta ba da ke gudana kuma ba su gamsu da shi a cikin jama’a da makotan su.
Ya nemi jama’a da su cigaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar nan da kasa baki daya.
” Abubuwan da ke faruwa yanzu, mu na fuskantar matsalar tsaro, wanda ke bukatar yin addu’o’in kawo karshen shi daga wajen jama’a “, a cewarsa.
Ya kara da cewar jami’an tsaro na bakin kokarin su, ina da tabbacin zaman lafiya zai dawo ba da jimawa ba a kasar nan.
A bayaninsa, babban limamin masarautar Kontagora, Mallam Shehu Rimaye wanda ya jagoranci sallar idin raka’a biyu, ya bayyana godiyarsa ga Allah akan abubuwan da su ka anfani da shi na watan Ramadan, ya roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.
Malamin ya yabawa kokarin jami’an tsaro akan yaki da ‘yan ta’adda da su ke yi a kasar nan.
Malam Shehu yayi kira ga al’ummar musulmi da su cigaba da yin addu’o’i, ya jawo hankalin talakawa da su daina zagin shugabanni. Haka ya nemi iyaye da su baiwa ‘yayan su kyakkyawar kulawa, ya nemi da su sanya idanu wajen hana ‘yayansu da yin fita wanda ba na addini ba.
Mai martaba sarkin Sudan na Kontagora, Alhaji Sa’idu Namaska da ya samu wakilcin madawakin Kontagora, Alhaji Aminu Ahmed
Gwamna Sani Bello ya ziyarci fadar sarkin bayan kammala sallar idin.

Exit mobile version