Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Dakatar Da Hakimin Badarawa

Zamfara

Daga Mahdi M. Muhammad,

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya dakatar da hakimin Badarawa a masarautar Shinkafi, Surajo Namakkah, saboda bayar da mukami ga wani jami’in soja da aka kama da sayar da harsasai ga ‘yan Bindiga.

Gwamnan ya ce, jihar ba za ta amince da duk wani abu da zai iya lalata zaman lafiyar jama’ar Zamfara ba.

Babban daraktan yada labarai na gwamnatin jihar, Yusuf Idris, ne ya sanar da dakatarwar a ranar Juma’a.

Gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da cewa duk wanda aka samu yana da laifi za a hukunta shi yadda ya dace.

Matawalle ya yi gargadin cewa, daga yanzu dole ne sarakunan gargajiya su nemi amincewa kafin su ba da wani mukami, don kauce wa abin kunya ga gwamnati da masarautar.

A cewar gwamnan, an kama jami’in sojin ne kwanan nan da harsasai 20 masu rai 62mm.

An kama wanda ake zargin a daidai lokacin da ya ke mika bindigogin ga wani Kabiru Bashiru na kauyen Maniya, masarautar Shinkafi, kuma ya karbi kudin N100,000 daga hannun ‘yan bindiga.

Gwamnan ya yaba wa hukumomin tsaro kan cafke wani Dakta Kamarawa wanda ke da kayan sojoji hudu da katin shaidar sojoji.

Ya ce, Kamarawa ya kware kan samar da kakin soji da magunguna ga ‘yan bindiga a Zamfara.

Matawalle ya nuna bakin cikinsa kan yadda wasu jami’an tsaro marasa kulawa suka shiga ayyukan ‘yan ta’adda, yana mai cewa hakan zai kawo cikas ga ayyukan da ake yi kuma hakan ba zai yiwu a kawo karshen ta’addancin a kasar ba.

Ya kara da cewa, “al’umma ba za ta ci galaba kan masu aikata miyagun laifuka ba a cikin irin wannan tsarin.”

 

Exit mobile version