Gwamnatin Neja ta sanar da sanya dokar takaita zurga-zurgan mashuna daga karfe goman dare zuwa shidda na safe a yakin garin minna da kewayenta.
Sanarwar wadda sakataren gwamnatin jiha, Ahmed Ibrahim Matane ya sanyawa hannu, ya gargadi masu sana’ar kabu-kabu wadanda da aka fi sani ‘yan Okada da masu tukin mashin a cikin garin minna da kewayenta da su guji daukar mutum sama da daya akan mashin a kowani lokaci.
Sakataren ya janyo hankalin masu tukin Keje-Napep da su guji daukar fasinja fiye da ka’ida, sanarwar tace dokar zai fara aiki ne ranar asabar din makon nan 15 ga watan Fabrairu wanda ya shafi takaita tukin mashin a wannan lokacin da aka ambata a baya ya zama wajibi a dauke shi saboda matsalar tsaro da jihar ke fuskanta a halin yanzu, wanda ya shafi tashin hankali da garkuwa da mutane tare da kashe karshen al’umma da mahara ke kaiwa jama’a, ta hanyar kai hare-haren makiyaya da garkuwa da jama’a.
Wajibi ne kowani dan kabu-kabu da masu tukin mashin mai kafa uku wato Keke-Napep da su mallaki lambar a ababen hawansu daga hukumar tara kudaden haraji ta jiha, wanda yai daidai da dokar sufuri ta jiha ta shekarar 2015 akan tsarin sufuri ta jihar Neja da aka yiwa gyaran fuska.
Jihar Neja wadda aka sani da zaman lafiya tsawon lokaci a kasar nan, yau tana fuskantar barazanar tashin hankali da kashe-kashen jama’a saboda hare-haren mahara masu dauke da makamai, ya zama wajibi a dauke duk irin matakin da ya dace wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, da zai samar da kwanciyar hankali tare da dakile hanyoyin da marasa gaskiya ke anfani da shi wajen cin ma burin su.
Sakataren ya cigaba da cewar matsalar tsaro da ake fama da shi a halin yanzu a jihar, ba abu ba ne da gwamnati za ta dunkule hannu tana kallo wanda ya zama barazana ga rayuwar ‘yan kasa, musamman wadanda abin ya shafa kai tsaye wadanda maharan suke auka ma wa, gwamna jiha, gwamna Abubakar Sani Bello yake dauka matakai dan magance shi, dan samun zaman lafiya da Kwanciyar hankalin jama’a.
Ahmed Matane yace gwamnati ba zata lamunci duk wani abu da zai kawo hargitsi ba wanda ya zama wajibi a takaita zurga-zurgan mashuna wadda kusan da shi ne marasa gaskiya ke fakewa wajen cin ma mugun nufinsu.
Takardar wadda jami’in yada labarai ofishin sakataren gwamnatin jiha Lawal Tanko ya rabawa manema labarai ranar alhamis, ta bayyana cewar sakataren yayi kira ga masu tukin mashin da Keke-Napep a cikin garin minna da kewaye da su dokokin da gwamnatin ta fitar wanda ta baiwa jami’an tsaro damar fara aiki akan sa daga ranar asabar domin duk wanda aka samu da karya dokar zai fuskanci hushin hukuma.