Tsaro A Jihar Zamfara: Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba

Sanin kuwane cewa ‘Gwamnatin Tarayya ce ke da Jami’an tsaro a fadin kasar nan kuma ita ke d alhakin tura su a cikin jihohi da kannan hukumomi.

Su Kuma jihohi da kananan hukumomi na taimaka wa jami’an tsaron wajen gudanar da ayyukansu .

Jihar Zamfara ta kasance shekaru bakwai ke nan al’ummar na cikin firgici da rahin natsuwa ba ma a cikin kauyuka ba har da manyan garuruwa irin su kananan hukumomi.

A cikin shekaru bakwai da suka gabata dubba rayuka  aka rasa da dukiyoyi masu yawa, musamman a garuruwan Ligyado da Kizara daTingar Baushe da’yan Warin Daji da Maradun da Shinkafi da Birnin Magaji.

Wannnan ne ya sa rundinar sojojin kasar nan ta kaddamar da rawar daji inda maharan suke cin karensu babu babbaka watau dajin Dansadau da rundinar ta kaddamar da rawar daji, don ganin ta share duk wasu masu kashe mutane da satar Shanu, karkashin jagorancin shugaban askarawan Nijeriya shugaban kasa Muhammad Buhari.

Tun da gabatar da wannnan rawar daji a watan bakwai na shekara ta 2016, abu kamar ya lafa ana ganin an magance matsalar ashe bako na bayan gari, ‘yan watanni da janye sojojin suka dawo suka ci gaba da ayyukansu na ta’addanci.

Sai ga shi maharan sun fito da wani salon kisan gila da garkuwa da mutane, inda su kai awon gaba da tawagar ‘yan kasuwa mutum arbain, cikinsu har da mataimakin shugaba karamar hukumar Anka, da wasu kansiloli.

Wannan ne ya sa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Abdul’aziz Yari Abubakar, ta kafa kwamitin sasanci wanda mataimakinsa Malam Ibrahim Wakala ke shugabanta da kuma kwamandan sojojin Kaduna da na Sakkwato da kwamishinan ‘yan sanda da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar tsaro.

Wannnan kwamitin ya yi  iya nasa kokarin wajen Samar da sulhu tsakanin ‘yan sa-kai da Fulani Wadanda Buharin Daji ke jagoranta. Kwamitin ya samu nasarar amincewa kowane bangare na cewa, subn yarda su ajiye makamansu, An gagarumin taro saboda murnar wannan sulhu, inda aka bukaci bangarorin su a jiye makaman na su a bainar jama’a, wanda aka yi a fadar Mai martaba sarkin Zirmi da Fadar Gidan Gwamnati jihar.

Kwamitin ya kammala aiki sa ne a cikin shekara da ta gabata inda aka yi biki jinjiwa manbobin kwamitin a Fadar gida gwamnati da ke Gusau Wanda Gwamna Yari Abubakar ya jagoranta.

Ana tunanin an kai karshen matsalar mahara da masu garkuwa da mutane sai kuma ga shi abin jiya ya dawo, inda a cikin makon da ya gabata ne, maharan suka dira a garin Goran Namaye inda su kashe mutane shida kuma suka yi garkuwa da ‘yan ‘yan dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bakura da Maradun Honarabul Yahaya Chado Goran Namaye, Jinaidu da Nasiru. Amma yanzu haka Nasirun ya dawo da labarai masu yawa a kan  maharan domin tataunawa a kan batun fansa. kuma yanzu haka shi ma Nasiru ya dawo sakamakon milyoyin Kudin da suka amsa a wata majiyar. A ranar Talata da ta gabata.

Domin tafiyar ta mu ta yi kyau bari mu waiwaya baya, a cikin watanni biyu da suka wuce mahara, sun kashe mutane a Danfako da Rantana da wasu da dama da ke cikin karamar hukumar Talata Mafara. Haka kuma a watanin baya ma a karamar hukumar Tsafe gungun mahara sun kai hari ofishin hukumar kiyaye hadura ta kasa da ke karamar hukumar Tsafe cikin jihar Zamfara, suka harbi kwamanda mai suna Mubarak Hamza, nan take ya ce, ga garinku nan kuma su kai awon gaba da abokin akinsa mai suna Muhammad Birnin kudu,suka shiga daji da shi.

Haka ma a cikin karamar hukumar Bukuyum sun kai hari a kauyukan Yashi da Buzuzu ‘yar jejeni suka yi awan gaba da shanu 1,500, da kuma mata biyar a kan cewa sai an ba su Naira miliyan biyar za su bada matan, amma a karshe, dai sai da aka ba su Naira miliyan daya da dubu dari hudu, sannan suka sako matan. Aminu Abubakar Ya shaida wa manema labarai,faruwar hakan.

A wata ganawa da sakataren Gwamnati jihar ya yi da ‘yan jarida a kan tsaro, ya ce, jihar ta rabawa jami’an tsaro, motoci dari hudi da ashirin da daya a cikin shekara shida da jagorancin Gwamna Abdul’aziz Abubakar Yari a jihar. Sakataren Gwamnatin Farfesa, Abdullahi Muhammad Shinkafi ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a majalisar dokokin Jihar.

Sakataren ya bayyana cewa’ Gwamnatin tarayya ta samar da bataliya guda ta masu jiran ko- ta-kwana ta ‘yan sada watau (Mobile Police Unit) a karin samar da tsaro a cikin jihar. Sai kuma sojoji dari bakwai da aka karo suna nan jihar Zamfara, kuma Gwamnati jihar karkashin jagoranci Gwamna Yari na hidimtawa da kakarinta ga jami’an tsaron don ganin an dakile dukkan wani aiki na  bata-gari da mahara.

A wata sabuwar kuma shugaban majalisar ta jihar Zamfara, Honarabul Sunusi Rikiji, da tawagar sa ta ziyarci garin Guza, da ke cikin karamar hukumar Talata Mafara da mahara suka kashe mutum biyar da kuma jikata wasu da dama.

Honarabul Sunusi Rikiji a jawabinsa na jajanta wa da ya yi, da addu’ar neman gafara ga wadanda aka kashen, sannan kuma ya ba iyalansu tallafin Naira 250,000, su kuma wadanda aka raunata Naira dubu dari 100,000 kowannensu. Daga nan sai ya tabbatar musu da cewa ya tabbatar masu da cewa Gwamnati na iyaka kokarinta na samar da tsaro a fadin Jihar Zamfara.

Rundinar ‘yansanda A Jihar Zamfara ta yunkoro wajan samun Sakwanini daga Bankunan Jama’a don kare rayukan al’umma ta hanyar raba kasidu da harshen Ingiishi da na Hausa. Kwamishinan ‘yansandan CP.Kenneth Ebrimson ya kaddamar da wannna kasidar a lokacin da yake gabatar da taron ‘yan jarida na karshen shekara a hedikwatarsu da ke Gusau.

Kwamishinan ya bayyana cewa’  don kare al’umma, rundinarsa ta samar da kasida mai dauke da lambobin jami’anta na Jihar don isar da sakon gaggawa a lokacin da ake fuskantar barazana daga miyagu.

Kuma wannan ya kafar Isar da sakonin gare mu zai taimaka wajan kare rayukan al’umma. Don gudun tsoro isar mana da sakon mutum na iya boye lambar wayarsa, ko kuma ya aika da sakon kar-ta-kwana, mu kuma da yardar Allah za mu bi didigin wannan sakon.

Kuma wannan kasidun za mu raba su ne a kasuwanni da tashoshin motoci da Kuma muhimman warare. Fatanmu shi ne mu samu hadin kan al’umma wajen kawo zaman lafiya a jihar Zamfara.

Lambobin sun hada da ta sai ce ta farko kwamishinan ,08164845090, sai ta jami’in hulda da jama’a na rundinar, watau PPRO,08091914752, sai kuma ta mataimakin kwaminan na shiyyar Gusau, 09063263315, na kuma Talatar Mafara,08126655441.da na Kauran Namoda, 08037702837, da dai sauran na DPO na kananan hukumomin duk kasidar na dauke da su.

Kwamishinan ya Kuma bayyana nasarorin da suka samu na kama masu garkuwa da mutane da ‘yan Sara suka ,da mahara da su ka addabi al’umma. Kuma yanzu haka rundunarsa babu dare ba rana ta tashi tsaye wajen dakile duk wasu miyagu da ‘yan ta’addan da ke naiman hana al’ummar jihar Zamfara zaman lafiya.

A kan haka ne ya mika godiyarsa ga al’ummar jihar Zamfara na hadin kai da suke bai wa rundinar.

Bayan wannan a makon da ya gabata ne Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar ya bai wa Jami’an tsaron wa’adi a kan su kamo wadanda ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a lokacin da ya je jajen ga al’ummar garin Goran Namaye. Kuma wannan wa’adin mako guda ne a cikin wannan makon yake cika.

Don haka gwamnan ya bayyana takaicinsa ganin yadda yake kashe milyoyin kudi a kan harkar tsaro kuma bai taba rage ko kwaboba ga abin da suka bukata.

A cikin wannan makaon ne a Litinin da ta gabata aka gudanar da taro da Gwamna da shugabaninin kananan hukumomi dan masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro a Talata. Shugaban kungiyar kananan hukumomi Honarabul Muhammad Umar Birnin Magaji ya bayyana wa ‘yan jarida a Gidan Gwamnati cewa: Wannan taron sun gudanar da shi ne kamar yadda suka Saba da mai daraja gwamna don inganta tsaro a cikin kananan hukumominmu.

 

 

 

 

Exit mobile version