Sagir Abubakar" />

Tsaro: Kowa Nada Rawar Da Zai Taka A Nijeriya – Kwamred Ruma

Shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Katsina, reshen (Trade Union Congress) Kwamred Muntari Abdu Ruma ya bayyana cewa kowa na da rawar da zai taka don ganin an kawo karshe n matsalar da wasu sassan kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Muntari Abdu Ruma ya bayyana haka ne, jim kadan bayan kammala nadin sarautar da Sarkin Ruma, Hakimin Batsari ya yi masa a jiya Juma’a, a matsayin Raya Karkaran Ruma Saboda irin jajircewarsa da kwazo da kuma irin gagarumar guddumuwar da yake bada da kawo cigaba a karamar hukumar Batsari da ma jihar Katsina baki daya.
Sabon Raya Karkaran Ruma, ya kara da cewa karamar hukumar Batsari na cikin mawuyacin hali, saboda idan ka cire Batsari da Wagini babu garin da za ka je cikin kwanciyar hankali, matsalar kusan ta tabarbarar da tattalin arzikinmu, makarantu da dama an daina zuwa ga noman ya faskara, amma Alhamdulillah an fara samun sauki. Wadannan na daga cikin dalilai da Sarkin Ruma ya ga ya dace ya kira mu ya sanya mu a cikin majalisarsa don ganin mun ci gaba da bada guddumuwar mu ta yadda za’a samu dawammamen zaman lafiya a karamar hukumar Batsari. A shirye nike na bada guddumuwata dari bisa dari.
Alhaji Muntari Abdu Ruma ya ci gaba da cewa kowa na da irin guddumuwar da za shi iya badawa, tun daga karami maaikacin ko karami dan kasuwa har zuwa kololuwar mataki to kana da guddumuwar da za ka bada, kuma ita ce al’umma suke bukata. Ina kira kowa ya tashi tukuru ya bada guddumuwar komin kankantarta. Saboda idan kowa zai bada tashi za ta taimaka wajen habbaka garinku da karamar hukumar ku da jihar dama kasa baki daya, kowanne dan Adam nada tattare da wata basira da Allah ya huwace Masa.
Daga karshe Ina mika godiya ta musamman ga maigirma Sarkin Ruma, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma, bisa ga zabo ni da ya yi bisa ga cancanta ya nada ni wannan sarautar Raya Karkaran Ruma, gaskiya na ji dadi kwarai, Saboda ni ba nema na yi ba, cancanta ta aka gani ta na dace, kuma zan ci gaba da taimakawa masu karamin karfi da kwato hakkin wanda aka zalunta. Ina mika sakon godiya ga wadanda suka samu halartar nadin sarautar da aka yi man a Fadar Mai Martaba Sarkin Ruma, Hakimin Batsari.

Exit mobile version