Sani Hamisu" />

Tsaro: Kungiyar Makiyaya Ta Bai Wa Gwamnonin Arewa Mafita 11

Kungiyar Fulani makiyaya mai suna Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN) ta zayyano wasu matakai  guda 11 da gwamnonin Arewa za subi domin magance matsalar rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewacin Najeriya, kuma ta bukaci a gaggauta aiwatar da dokar a kasa.

Wannan na zuwa ne a cikin wata takarda da shugaban  kungiyar Khalil Mohammed Bello, ya sanyawa hannu ranar Laraba a garin Damaturu babban birnin jihad Yobe, ya ce “wannan rikici wanda kullum yake tasowa a Arewacin kasar nan sakamakon rashin nasarar da gwamnonin jahohi suka yi hakan ta kara sanya ci gaban rikicin kullum sai kara zama sabo fill yake.”

Shugaban ya kara da cewa” rashin tsaro ya zama wani abun dubawa a Arewacin kasar,mussamman ma lokacin da masu sace-sace, ‘yan bindiga masu tada zaune tsaye, inda suka sake farfado da ayyukan su a wurare daban-daban a jahohin.”

Ya kara da cewa wadannan matsalolin rashin tsaron wadanda suke faruwa sun zama kalubale ga matsalar rashin tsaro a Arewacin yankunan sassa na kasar.

“Abu mafi muni shine yadda kungiyar Boko Haram suke gudanar da ayyukan su, ga kuma masu garkuwa da mutane wadanda suka addabi jahohin, rikici tsakanin Manoma da makiyaya, bugu da kari ga rikicin addini wanda ya maye kusan duk kan jahohin Arewacin Najeriya mussaman ma rikici tsakanin kabilu da yankunan su.” in ji Bello.

“Saboda haka, kungiyar Fulani sun yanke shawarar cewa za su bi duk wasu hanyoyi wajen ganin zaman lafiya ya wanzu a fadin kasar, kuma akwai bukatar gwamnoni guda 19 na Arewa da su kara sanya  idanuwan su akan wannan lamarin, wajen kare rayukan jama’ar su dabbobin su dama makarantun su da kuma inganta wuraren da abubuwan yake faruwa.

“Sauran batutuwa da kungiyar ta zayyano su Idan aka bisu yadda suke a yankunan to za a samu nasarar kawo karshen tashe -tashen hankula kamar irin su kafa wajen shan ruwa na dabbobi, rarraba kayan kiwo ga makiyaya, da kuma samar da ruwa a cikin yankunan karkara.”

Tsarin yadda za a magance rashin zaman lafiyar  shugaban kungiyar Fulani Khalil Mohammed Bello ya fade su kamar haka:

1. Tsaro ga mutane da suke kiwo da dabbobin su a fadin kauyukan da suke rayuwa a Arewacin kasar.

2. A samar musu da Makarantu na musamman wadanda zasu rinka koyar dasu abubuwan da suka shafi zamani.

3. Tattaunawa akan ci gaban kiwo a karkara tare da magance matsalolin da yake damun su.

4. Gina wajen da  dabbobi za su rinka kiwo tare da mutane da zasu rinka kula da su, kuma a horar da su ayyukan kiwo na zamani.

5. A rinka kula da  tsarin dabbobinsu.

6. A  taimaka musu da abinci na dabbobi da za su rika ci cikin watan Maris zuwa watan Yuni.

7. Bayar da ruwa mai tsafta don amfanin mutane da dabbobin.

8. Gina wajan da matasa zasu rinka gudanar da al’amuran su na yau da kullum domin hana su aikata laifukan sace-sacen mutane.

9. Gabatarwar shirin karfafawa ga masu kiwo dabbobin a matsayin madadin rayuwa.

10. Maimaita sake fasalin duk dabbobin shanu da  katange su saboda aiwatar da ayyukan cigaba don hana masu garkuwa yin lalata a yankunan manoma.

11.  Samar da tsaro da zaman lafiya tare da tattaunawa a tsakanin ‘yan adawa da ke cikin Arewacin.

“Mu na so mu jaddada cewa, wadannan sune matakan da KACRAN ta yi nazari akan su kuma ta bada shawara ga gwamnoni Arewa da su bi wannan shawarar wajen wanzar da zaman lafiya a dukan yankin Arewa dama Najeriya baki daya domin inganta tattalin arzikin kasarmu, “in ji kungiyar.

Exit mobile version