Tsaro: Matakan Da Suka Taimaka Mana Wajen Kare Al’umma Da Makarantunmu – Gwamnan Gombe

Rikicin Kabilanci

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewar gwamnatinsa ta hada guiwa da kungiyoyin addini da na al’umma ciki har da sauran masu ruwa da tsaki har da Sarakunan gargajiya domin taimaka mata wajen tabbatar da inganta tsaro gami da dakile ‘yan matsalolin tsaro da suke addabar jihar.

Inuwa wanda ke bayyana hakan a ranar Litinin, a sa’ilin da ke ganawa da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa biyo bayan wani tattaunawar da suka yi da shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidan gwamnatin Nijeriya da ke Abuja.

A cewar gwamnan, kasancewar yadda jihar ta zama a tsakiyar jihohin arewa maso gabas, hakan ya janwo wasu ‘yan matsalolin tsaro, amma a bisa kokarin hukumomin tsaro da hadin guiwar al’umma ana samun habaka zaman lafiya da kwanciyar hankali mai inganci matuka.

Ya ce: “Muna tsakiyar Arewa Maso Gabas, saboda mun yi iyaka da dukkanin jihohi biyar da suke wannan shiyar, a sakamakon hakan, ‘yan matsalolin tsaro, tasirin Boko Haram da sauran rikicin manoma da makiyaya sun kasance kalubalen da suka addabi Gombe a da baya.

“Amma bisa tashinmu tsaye da yin aiki tukuru babu dare ko rana tare da hadin guiwar hukumomi, sarakuna, limamai, shugabannin al’umma, jami’an tsaro, mun yi kokarin samar da kyakkyawar fahimtar juna a tsakanin al’ummominmu.

“Zan iya cewa, muddin aka kwatanta Gombe da sauran Jihohi, za a iya cewa Gombe tana cin gajiyar zaman lafiya sosai, don haka muna godiya wa Allah, muna godiya wa jama’anmu da masu ruwa da tsaki a bisa hadin kai da goyon bayan da suke bamu.”

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan garkuwa da dalibai a sassan wasu jihohi, Gwamna Inuwa ya bayyana cewar bayan nazartar halin da ake ciki na galabaitar da yara dalibai, nan take gwamnatinsa ta dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da kariya ga dukkanin makarantun da suke jihar da dalibai.

“Mun nazarci halin da ake ciki don haka muka janyo jami’an tsaron cikin gida, ‘yan Banga, Bijilante domin yin aikin yadda za mu tabbatar da kare makarantunmu daga dukkanin wani hari.

“Fiye da dukkanin abubuwan da muka yi wa sha’anin tsaron makarantunmu mun ga natija domin kuwa an samu matakan kariya da kwanciyar hankalin dalibai da makaratunmu, jami’an tsaro sun sanya ido kan makarantu domin tabbatar da kariya a kowani lokaci.

“Wannan ya bamu sa’a aka samu kwanciyar hankali a cikin makarantu da kuma kare jama’an jiharmu, muna godiya wa Allah Madaukakin Sarki bisa wannan natija,” ya shaida.

Gwamna Inuwa, sai ya sha alwashin bunkasa wadannan matakan da gwamnatinsa take bi da ya jawo inganci tsaro da kwanciyar hankalin jama’a, yana mai kuma cewa za su kara jawo masu ruwa da tsaki musamman sarakuna da limamai, jami’an tsaro domin ganin haka ta cimma ruwa na kyautata tsaro a dukkanin matakai.

Exit mobile version