Shugaba kuma Mawallafin kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yi kira da a kara ingantawa da samar da hadin kai da kawancen juna a tsakanin ’yan jarida da gwamnati wajen dakile matsalolin tsaro da suke addabar Nijeriya.
Ya kara da cewa, tabbas ’yan jarida abokan tafiya ne wajen kyautata lamuran tsaro da kuma bayar da gudunmawa a kokarin yaki da ’yan ta’adda da masu tayar da kayar baya da ke hana jama’a barci da minshari sakamakon ayyukan ta’addanci.
Malagi yana jawabi ne a yayin bikin ‘Makon ’Yan Jarida’ na shekara-shekara da reshen kungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) a Jihar Neja suka shirya a ranar Asabar din karshen wancan makon a garin Minna, babban birnin jihar.
A matsayinsa na babban bako a yayin taron ya yi bayani kan mukala mai taken ‘Gidajen Jaridu Da Matsalar Tsaro A Nijeriya: Hangen Jihar Neja Kan Rawar Da ’Yan Jarida Ke Iya Takawa Don Dafa Wa kokarin Gwamnati Wajen Kawo karshen Matsalar Tsaro A Nijeriya’.
Ya lura da cewa, ’yan jarida “suna da gagarumar rawar da za su iya takawa a gwagwarmayar dakile munanan dabi’u da matsalolin da suke damun kowa da ke hana jama’a barci.”
Mawallafin, wanda ya samu wakilcin tsohon Babban Sakataren Gwamnan Neja kuma Editan Lamuran Tsaro na Blueprint, Jibrin Baba Ndace, yana cewa, “dole ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro suka addabi kasa gidajen jaridu, gwamnatoci da hukumomin tsaro a dukkanin matakai da masu ruwa da tsaki da su kasance a layi guda wajen tunkarar matsalar.”
Ya gargadi ’yan jarida da su ke bada rahoton harkokin tsaro bisa takatsantsan, bisa kwarewa da bin dokoki da ka’idojin aiki, domin kauce wa ingizawa da kawo cikas ko nakasu ga hukumumin tsaro a kokarinsu na yakar kalubalen tsaro.
Yana mai cewa, a halin hakan, ba wai ‘yan jarida za su sauka daga kokarin bin layin ‘yancin gudanar da ayyukansu na jarida ba ne, a matsayinsu na masu sanar da al’umma halin da ake ciki, akwai bukatar su bada karin gudunmawa ne wajen tallafa wa dukkanin kokarin gwamnati da masu ruwa da tsaki wajen kawo karshen matsalar tsaro da ake cigaba da fama da shi a wannan kasar ta hanyoyin inganta aiki da yin labaran da suka dace.
Alhaji Malagi ya kara da cewa: “Gidajen jaridu da al’umman kasa dole ne su tashi tsaye wajen tunkarar matsalar tsaron da ke addabar kasa ta hanyoyin da za su iya bada nasu gudunmawar.”
Daga nan, sai ya jawo hankalin ‘yan jarida da sauran wadanda ke aiki a gidajen jaridu da suke rungumar aikin da ke gabansu tonawa da yakar matsalar tsaro da Nijeriya ke fuskanta.
Alhaji Idris wanda kuma shine sakataren kungiyar mawallafa jaridu na kasar, NPAN, ya bada shawarar cewa za a iya kara inganta aikin jarida a kasar nan ta hanyar bada horon da karin sani kan ‘yan jaridan da ke aiki domin kyautata musu aikinsu, yana mai cewa dole ne kuma dukkanin hukumomin tsaro su amince kan cewa ‘yan jarida abokan jerensu ne ta fuskacin nemo mafita kan matsalolin da suke jibge.
Ya kuma ce, a daidai lokacin da dan jarida ya dauki alkalaminsa zai yi rubuta, ya fara tunanin ra’ayi da muradin kasa kafin rashin kashin kansa domin ta hakan ne zai iya bada gudunmawa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar nan.
Kakaki Nupe ya nemi gwamnati da jami’an tsaro da su nuna kwarin guiwarsu kan ‘yan jarida a fannin bada rahotonnin da da suka shafi tsaro, tare da taimaka wa ‘yan jaridan wajen sauke nauyin da ke kawukansu ko basu damar gudanar da ayyukansu cikin sauki ba tare da wani tsangwama ba.
Ya ce, jaridarsu ta Blueprint da sabuwar da suka fara bugawa ta hausa mai suna Manhaja suna bada gagrumar gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiyar kasar nan, yana mai cewa suna kuma da gidan rediyo da kokarin kafa gidan talabiji dukka a kokarinsu na cigaba da bada gudunmawa domin cigaban Nijeriya da wanzuwar zaman lafiyarta.
Alhaji Idris Malagi a matsayinsa na babban mai kaddamarwa, ya bada gudunmawar naira miliyan daya.
Sauran fitattu kuma gogaggun mutanen da suka halarci taron sun hada da: wakilin gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, (Alh Yusif Suleiman, kwamishinan albarkatun Ruwa); shugaban kungiyar ‘yan jarida na kasa (NUJ) Mista Chris Isiguzo; shugaban NUJ reshen jihar Neja, Malam Abdul Idris; wakilin shugaban taron, Injiniya Sani Ndanusa , Marafa Nupe (MaL Mohammed She, Ma’ajin NUJ na kasa).
Sauran su ne: mataimakiyar gwamnan babban bankin kasa Hajiya Aisha Ahmed, wacce Dakta Zainab Ndanusa ta wakilta; Alh. Muhammad Kudu Usman, Daraktan kudi na ma’aikatar lafiya ta kasa; Alh. UT Usman, Darakta Janar na hukumar fansho ta jihar Neja; Alh Danladi Buhari, tsohon babban sakataren ofishin SSG da sauran kusoshi.
Gwamnatin Gombe Ta Sanya Dokar Hana Fita A Garin Balanga
Daga Khalid Idris Doya, Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar dokar...