Connect with us

TATTAUNAWA

Tsaro: Mun Taka Muhimmiyar Rawa A kasar Nan –Babban Hafsan Sojojin Sama

Published

on

AIR MARSHAL SADIKUE ABUBAKAR shi ne Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya (NAF). A cikin wannan tattaunawar da ya yi da LEADERSHIP, wacce Wakilinmu MUHAMMAD MAITELA ya fassara, Babban Hafsan ya warware zare da abawa game da harkar tsaron Nijeriya da irin muhimmiyar gudumawar da su ke bayarwa wajen tabbatar da tsaron. Ya kuma tabo muhimman nasarorin da ya samu tun farkon kama aikinsa a matsayin Babban Hafsan mayakan sama, kana kuma ya shaida cewa ya na da kyakkyawan fatan sauke nauyin da ya hau kansa a matsayin mutumin da ya bauta wa kasarsa tukuru. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Shin wadanne kudurori ka ke da su a lokacin da ka kama aiki a matsayin Babban Hafsan Sojojin Sama?

Manyan kudurorin da na ke da su, su ne in tabbatar da cewa, na dora rundunar sojojin saman Nijeriya kan madaukakin matakin kwararru da bin ka’idar aikin tsaro. kwarewar da nake nufi ita ce, samun nagartaccen ilimin da yake hade da kwarewa. Sannan kuma da bukatar sanin ka’idar aikin, tare da biyayya irin ta gidan soja, wanda mun kudurci samun nasarar hakan ne ta hanyar bunkasa tunani da ilimin jami’an mu, ta amfani da bangarori daban-daban. Saboda haka ne ma ya sa na ambaci kwarewa tare da bin ka’idar aikin gidan soja a matsayin bangaren da zan fi mayar da hankali. Har wala yau kuma, a kan hakan ne ya jawo mu ka tsara cewa lalle dole akwai bukatar kara bunkasa kwarewar, tare da danfara shi da bin ka’idojin, wanda ta wannan ne jami’an mu za su iya gudanar da ayyukan tsaro cikin tsanaki, a makamancin wannan lokaci na kalubalen tsaro da mu ke fuskanta.

Wanda ala-dole mu kasance a tsanake, wanda ta hakan ne kawai za mu cimma nasarorin da mu ke da fata. Haka zalika, aiki cikin kwarewa da tsanaki ya na da mashahurin muhimmanci, saboda yadda mu ke fuskantar karancin kayan aiki a kasa, idan an kwatanta da abin da yake a kasa. Baya ga hakan kuma, a duk lokacin da kake gudanar da aikin ka, dole ka kwana da sanin cewa duk shirin da ka yi, shi ma abokin gaba a shirye yake ya yi amfani da kowace damar da yake da ita wajen ganin ya kawo maka cikas, wanda bisa ga wannan ne, kwarewa ce kawai babban matakin shawo kan matsalar tsaron da mu ke fuskanta. Wanda kuma bisa ga zahiri ita ce turbar da mu ke a kai shekara biyar da su ka gabata, kuma ta wannan bangaren za mu iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu. Sannan kuma abin da zan ce kan wannan shi ne, ina matukar jin dadin yadda mu ke samun gagarumin cigaba tare da nasarori.

 

Yallabai, wane tubali ka tarar a kasa da zai tallafa maka wajen cimma wannan manufa?

Na tarar da yunkuri da dama, saboda tun kafin in zo, wadanda su ka gabace ni sun yi ta kokari tare da mayar da hankali a kan muhimman abubuwa da dama wajen sauya fasalin rundunar sojojin saman Nijeriya. Wanda a shekarar 2015, Kwamandojin yaki guda hudu wadanda mu ka sauya musu fasali, tare da daukar ingantattun matakan sake bunkasa rundunar sojojin saman Nijeriya, da la’akari da yanayin yadda tsarin ta yake idan an kwatamta da kalubalen tsaron da Nijeriya ke fuskanta a yau. Wanda sauya fasalin kadai ba zai wadatar ba har sai ya dace da buwatun da ake da su a zamnance, da makamantansu. Wanda a karshen binciken, mu ka cimma matsayar cewa ba sauya fasalin ne kawai abin bukata ba, idan an yi la’akari da yanayin kalubalen da mu ke fuskanta ba.

Wanda bisa ga hakan, akwai bukatar karin wasu Kwamandoji ne, tare da samun ingantaccen horon kwarewa a salon yadda za a fuskanci yakin sama da na kasa a lokaci guda, ta hanyar kafa cibiyar da za ta bayar da horon yaki ga sojojin sama (ATC) da na kasa (GTC), yayin da jami’in da zai kula da cibiyar horas da dabarun yakin kasa kuma shi ne zai sanya ido wajen bayar da horon dabarun yaki ga sojojin saman, matakin farko na horas da tukin jirgin yaki, da horas da matakin farko kan tuka jirgi mai saukar ungulu, hadi da bayar da horon gaba-da-gaba, da makamantansu. Wannan shi ne matakin da mu ka dauka daga farko, sannan kuma a 2015 mun cefano na’urarorin sadarwa don bunkasa yanayin ayyukan tsaro. Wannnan ko shakka babu zai taimaka wajen taka muhimmiyar rawa a bangarori da dama, a karkashin kulawar kwararrun jami’an da su ka dace su kula da gudanar da wajen, wanda ya kunshi sassa biyu; bangaren kayan aikin sadarwa tare da tsarin sadarwa na zamani (CIS). bangaren tsarin sadarwa na CIS ya kunshi abubuwa masu alaka da harkokin sadarwa na zamani ICT, wanda ya shafi tattaro bayanai kai tsaye tare da daukar hotuna daga jirgin sama, da makamantan su.

Wannan daya ne daga cikin matakin da shalkwatar tsaron sama ta dauka, sannan kuma akwai bukatar duba yuwuwar samar da wani bangare na musamman dangane da tsarin kiwon lafiya, yayin da mu na kokari wajen ganin mun samar da shirye-shiryen da su ka shafi ayyukan kiwon lafiya. Haka kuma wannan ya samu ne ta dalilin bukatuwar da ake da ita wajen fadada ayyukan kiwon lafiyar. Yayin da a halin da ake ciki yanzu, mu na da asibitocin duba majinyata a matakin farko. Mun kafa daya a jihar Bauchi, akwai wani a Daura, tare da karin wani asibiti daya da mu ka fadada a Fatakwal. Haka zalika kuma, mun fadada kayan aiki a baki dayan asibitoci tare da cibiyoyin kiwon lafiya na rundunar sojojin saman Nijeriya. Wanda kuma bisa ga hakan, akwai bukatar canja kayan zuwa inda su ka dace domin samun cikakkiyar kula. Bugu da kari kuma, yakin da mu ke yi da matsalar tsaro, wanda hakan ya tilasta dole mu yi amfani da matakai tare da hanyoyi daban-daban, a yaki da matsalar tsaron. Kuma wannan ya na da bambanci da nazariyyar da Kinetic ke yi wajen fuskantar abubuwa, da ya shafi bayar da tallafin kiwon lafiya ga ‘yan gudun hijira hadi da sauran al’ummar da ke zaune a yankunan da rikicin ya yi kamari. Har wala yau kuma, yin hakan ya zama dole, saboda la’akari da mu ka yi dangane da yaki da matsalar tsaro, ya na da bukatar samun cikakken goyon bayan al’ummar da su ke zaune a yankunan da ake aikin samar da tsaron, kuma zai yi wahala ka samu cikakken goyon bayan matukar ba ka kirkiro musu wasu hanyoyin da za sa su taimaka musu ba, wanda bisa ga wannan ne mun yi kokarin wajen fuskantar wasu matsalolin su ta fannin samar da asibitocin jeka-ka-dawo a yankunan su. Haka kuma, ko shakka babu wannan hanyar da mu ka dauka ta taimaka mana sosai. Sannan kuma mun dauki matakin fuskantar wasu matsalolin su, ma su alaka da rundunar sojojin sama. Kuma mu na da bukatar barikin sojojin sama a wajen, wanda kuma mu na aiki a kai, duk da matsalar kudade tare da wasu matsaloli na daban, wadanda ba za mu iya tunkarar su a lokaci guda ba. Ta bangaren gudanar da tsare-tsare kuma, akwai bukatar makarantar koyon tukin jirgin sama, wanda a Kaduna, mu na da jirage guda uku ne kacal, kuma sun yi wa dalibai 40 zuwa 50 kadan wajen koyon tukin jirgin sama.

Zancen da nake magana da kai yanzu, jirage 15 ne kadai su ke tashi a tsarin koyon jirgin sama. Wadanda jami’an sojojin sama su ka samu horo, wanda wadannan jami’an horon da su ka samu ya zarta wanda su ka yi a Kaduna, a horo a matakin farko a Kano da ya dauki kimanin shekara hudu da rabi ko makamantcin hakan, kuma mun horas da kwararrun direbobin jirgin sama 318, baya ga hakan kuma da karin wasu da su ka samu horo a fanni na daban, wanda takwarorin mu su ka gudanar da kwangilar ta hanyar wasu kasashen Morocco da Misra. Sannan kuma, rundunar sojojin kasar Misra (Egyptian Air Force) ta horas da adadi mai yawa na mayakan mu na jiragen sama, hadi da ita ma kasar Morocco ta horas da adadin mai yawan. Wanda su ka ba mu cikakkiyar damar tura jami’an mu don samun horo na musamman dangane da kwarewa a tukin jirgin sama, inda mun samu damar tura mutanen mu zuwa can don koyon tukin jirgi mai saukar ungulu a kasar Azerbaijan.

 

Ka zo a lokacin da matsalar Boko Haram ta yi kamari. Ta ya ka tunkari lamarin?

A iya fahimtata, sojojin saman Nijeriya sun taka muhimmiyar rawa a fannin yaki da mayakan Boko Haram. Wanda ta la’akari da yanayin fadin yankunan, wanda jirgi ne kawai zai tunkarar su ba tare da wahala ba, sannan kuma mu na aiki kafada da kafada da sojojin kasa. Sannan kuma, mu na tafiyar kimanin awanni 30,000 domin ganin mun bayar da cikakken goyon bayan da sojojin kasa ke bukata, wajen sammun tabbacin sun samu nasara ga makiyan su. Kuma idan za ka tuna, kafin shekarar 2015, akwai mayakan Boko Haram ko’ina, inda hatta a birnin Abuja su na iya shiga tare da kai harin bam a shalkwatar yan sanda Baya ga wannan kuma, sun kai harin bam a Plaza a tsakiyar birnin na Abuja. Haka kuma sun kai wani a Cocin Catholic a Madalla. Haka kuma sun dana wasu bama-bamai biyu a tashar mota a Nyanya, kamar yadda su ka tayar da wani bam a ofishin jaridar ‘This Day’ a Abuja. Bugu da kari kuma ga yadda su ke tayar da bama-bamai a kowane yankin kasar nan, wadanda su ka hada da Kano, inda su ka tayar da bam a babban masallacin Juma’a, wanda su ka kashe sama da mutum 200. Ga jihohin Kaduna, Plateau da Bauchi, inda su ka aiwatar da kai hare-haren ta’addanci, ciki har da gidan yari, kuma su ka kashe dimbin jama’a, lamarin da ya jawo kamarin al’amarin Boko Haram a lokacin. Haka zalika kuma, dubi yadda su ka mamaye wasu yankunan Arewa maso Gabas tare da kafa shalkwatar su a garin Gwoza, inda su ka sanya tuta da wuraren da su ke gudanar da mulki. Wanda har ya kai su na tikasta wa mutane biyan haraji da zartas musu da hukunci da makamantan su.

Amma bayan da aka zabi wannan gwamnatin, ya taimaka sojoji sun yi kokarin cin karfin ‘yan ta’addan. Duk wadannan nasarorin sun samu ne ta dalilin cikakken goyon bayan da gwamnatin tarayya, musamman ta bangaren bayar da dukan abin da ake da bukata a fannin yaki da wannan matsalar ta tsaro. Wanda a halin da ake ciki yanzu, kusan manyan ayyukan samar da tsaro a Arewa maso Gabas sun fi yawa a dajin Sambisa tare da bangaren zirin Tafkin Chadi, wanda yake kan iyaka da kasashen Chadi, Nijar da Kamaru. Kuma mun gudanar da ayyukan kwararru kan kudurin da mu ke da shi wajen cin karfin maharan, tare da bin diddigin yadda kai-komon su ke wakana a wadannan yankunan. Haka kuma, mun zagaya kimanin kilo mita 159,000 wadanda yake bukatar cikakken sanya ido.

Har wala yau kuma, mun samar da kayan abinci, kayan yaki, magunguna kuma mun dauke wadanda su ka samu raunuka zuwa birnin Maiduguri ta hanyar jirage ma su saukar ungulu. Sashe na daban kuma wanda mu ka bayar da gudumawa wajen sufurin kayan yakin sojoji daga Maiduguri, ta hanyar amfani da jirgi kirar C130H. Haka kuma mun taimaka wa gwamnatin tarayya a shirin raba kayan abinci, ta hanyar zirga-zirgar kayan abinci da jiragen sama a birnin Maiduguri, baya ga yadda matsalar tsaron ta tagayyara ayyukan noma. Haka kuma, mun bayar da cikakken goyon baya ga sojojin kasa, a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, a aikin tsaro. Wanda rundunar sojojin sama za su ci gaba da gudanar da irin wannan hadin gwiwa. Sannan kuma, bisa ga wannan, abinda zan kara tabbatar wa shi ne, mun taka muhimmiyar rawa tare da aiki tukuru.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: