Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Tsaro Na Barazana Ga Bunkasar Tattalin Arziki, In Ji Adedipe

by
10 months ago
in KASUWANCI
2 min read
Adedipe
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Babban mai ba da shawara a kamfanin ‘B. Adedipe Associates Limited’, Dakta Biodun Adedipe, ya ce, Nijeriya na da gagararriyar dama ta dace da fadada yawan mutane da bunkasar tattalin arziki a wannan shekarar, amma ya yi gargadin cewa yanayin tsaro na iya dakile yiwuwar hakan.

 

Samar da kaya ya kasance baya da yawan karuwar jama’a, wanda ya kai kimanin kashi 2.58 a cikin shekaru goma da suka gabata, a cikin shekaru uku da suka gabata.

Labarai Masu Nasaba

Kimanin Masarar Naira Biliyan 30 Aka Yi Asara Sakamakon Matsalar Tsaro A 2020 – Manoma

Gwamnati Ta Zargi ‘Yan Nijeriya Mazauna Waje Da Taimaka Wa Nakasa Attalin Arziki

 

Tare da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da hukumar kididdiga ta kasa (NBS), suna sanya kimar bunkasar bana zuwa kashi 2.5 da kashi uku bisa dari, Adedipe ya ce, tattalin arzikin na iya daidaita da karuwar mutane a 2021 idan an magance kalubalen tsaro cikin gaggawa.

 

Masanin tattalin arzikin, wanda ya yi magana a wajen taron karawa juna sani na wata-wata na kungiyar masu ba da rahoto kan harkokin kudi na Nijeriya (FICAN), ya ce, bankunan kananan kudade sun kasance hanya mafi tabbaci wajen gina tattalin arziki mai zorewa, amma ya nuna damuwa kan rashin gudanar da ayyukan kananan hukumomi.

 

A cewarsa, babbar manufar bude kananan sana’o’in zai kawo karshen matsalar rashin aikin yi a kasar.

 

Dangane da ayyukan banki, ya bayyana cewa, “bankunan Nijeriya sun kasance suna sanya ruwa sosai a cikin shekaru biyar da suka gabata, musamman a cikin shekaru biyu da suka gabata inda suka ninka ninki biyu na kason kudin da aka tsara.”

 

“Tare da rarar bashin zuwa ajiya wanda ya kai kashi 70.4, bankunan sun kasance kasa da yadda aka tsara, sama da wannan, za a iya daukarsu masu yawa. Saboda haka, bankunan suna da sararin fadada lamuni. Kalubale kuwa shi ne yadda za a iya fuskantar hadari musamman a rancen, musamman wajen bayar da rance ga kanana da matsakaitan masana’antu (MSME),” in ji shi

 

Adedipe ya kara da cewa, bankin Nijeriya ya kasance na biyu a Kenya wajen kirairar fasahar hada-hadar kudi amma hakan na shirin zama ta farko a nahiyar nan da ‘yan shekaru masu zuwa sakamakon saurin bunkasar da ake yi a yanzu.

 

Ya gargadi masu hannu da shuni da su jajirce don gasar da ta fito daga bankunan gefe, saboda haka suka zama ba su da wata ma’ana.

 

“Duniyar da bankunanmu suka yi aiki a cikin wata annoba ta pre-COBID-19 tana saurin bacewa. Wannan shine dalilin da ya sa muke tambaya menene ya kamata ya canja don bankunanmu su kasance cikin shiri don duniyar bayan Korona? ya tambaya.

 

Yana mai jaddada cewa, masu banki suna bukatar sabon tunani da hadin kai don tseratar da tattalin arziki daga mawuyacin hali.

 

Ya bayyana banki mai kula da zamantakewar al’umma a matsayin wanda ke magance kalubalen da aasar ke fuskanta, kamar talauci, rashin aikin yi da rashin tsaro.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

OLYMPICS: ‘Yan Wasan Nijeriya Sun Sauka A Birnin Tokyo

Next Post

Sallah Biki Daya Rana

Labarai Masu Nasaba

Manoma

Kimanin Masarar Naira Biliyan 30 Aka Yi Asara Sakamakon Matsalar Tsaro A 2020 – Manoma

by
10 months ago
0

...

Gwamnati

Gwamnati Ta Zargi ‘Yan Nijeriya Mazauna Waje Da Taimaka Wa Nakasa Attalin Arziki

by
10 months ago
0

...

Bankuna

Kasuwanci Na Raguwa Ne A Nijeriya Sakamakon Matsalar Tsaro – CBN

by
10 months ago
0

...

Bankin Duniya

Abubuwa 10 Da Babban Rahoton Bankin Duniya Ya Bayyana Game Da Nijeriya  

by
10 months ago
0

...

Next Post
Sallah Biki Daya Rana

Sallah Biki Daya Rana

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: