Daga Hussaini Yero,
A kokarin da rundunar ‘yan sanda ke yi na yaki da ‘yan ta’adda da suka addabi jihar Zamfara, yanzu haka Sufeton ‘yan sanda na kasa (IG) Muhammad Adamu, ya sake turo dakarun rundunar ‘yan sanda ta “Puff Adder 275” zuwa jihar Zamfara don kara karfafa yaki da ‘yan bindiga da masu tada kayar baya a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan, CP Abutu Yaro ne ya kaddamar da rundunar a sansani na 42 na rundunar ‘yan sanda kwatar dar da tarzoma da ke Gusau.
Kwamishinan ya bayyana cewa, wannan runduna shugaban ‘yan sanda na kasa ne ya kaddamar da ita a ranar 15 ga wannan wata a Abuja, kuma ya turo wa jihar Zamfara nata kaso don ganin an dakile ayyukan ‘yan ta’adda.
Shi ma anasa jawabin, Kwamandan runduna Puff Adder, Musa Abdullahi ya tabbatar da cewa, dakarun su za su yi iya kokarinsu wajan yaki da ‘yan ta’adda da bisa bin doka da oda alokacin da suke gabatar da ayyukan su.
Anasa jawabin Gwamna Bello Muhammad Matawalle Maradun da ya samu wakilcin, Kwamishinan tsaro, Hon Abubukar Dauran,ya bayyana cewa, al’ummar jihar Zamfara na godiya ga shugaban ‘yan sanda na kasa da ya sake turo Runduna “yan sanda karo na biyu a wannan Jihar ta mu.kuma duk abunda ya kamata muyiwa wadannan ‘yan sanda don samun nasara aikin su za mu yi da yardar Allah.