Nasir S Gwangwazo" />

Tsaro: Wa Ya Fi Gaskiya Tsakanin IBB Da Shehu Sani Kan Buhari?

A shekaranjiya ne a ka samu kace-nace ko kuma mu ce cece-kuce tsakanin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), da dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, a kan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Tun da fari dai, wato a ranar Talatar da ta gabata, IBB ya shaida wa taron manema labarai a fadarsa da ke garin Minna cewa, ya na da tabbacin cewa, Shugaba Buhari zai iya cika alkawarin da ya dauka na kawo karshen matsalolin tsaron da su ka addabi fadin Najeriya, kamar yadda ya daukar wa ’yan Najeriya alkawari a lokacin yakin neman zabe.

To, amma jim kadan bayan hakan sai Sanata Sani ya mayar da martani ga tsohon shugaban a Twitter, ya na mai nuni da cewa, ya daina bata lokacinsa wajen bai wa ’yan Najeriya irin wannan tabbaci kan mutumin da ba ya nuna ko a jikinsa kan halin da a ke ciki.

IBB, wanda ya kira taron manema labaran ne, don murnar bikin Karamar Sallah, ya nanata cewa, “Buhari ya na da karfi da kwarewar da zai iya fuskantar kalubalen da ke gaban Najeriya kuma ya maganta su, amma akwai bukatar ’yan Najeriya su kara hakuri da shugaban kasar.

“Buhari ba mutum ne wanda ya fi sabawa da zance na fatar baki kawai ba; mutum ne shi wanda a ka san shi kan fada da cikawa.”

Sai dai kuma a yayin da Sanatan ya ke tofa albarkacin bakinsa ga tsohon shugaban kasar cikin girmamawa, ya rubuta cewa, “Kawunmu IBB ya na buga kuge ne kawai ga kurma.”

Idan dai za a iya tunawa, muhimmin abinda a ka gudanar da yakin neman zabe da shi a babban zaben najeriya na shekara ta 2015 shi ne batun matsalar tsaro, inda Buhari ya yi alkawarin kawo karshen matsalar matukar an zabe shi a kujerar shugabancin kasar.

Burinsa ya cika, domin kuwa al’ummar Najeriya sun kada ma sa kuri’ar da ya kawar da shugaba mai ci a wancan lokaci, Dr. Goodluck Ebele Jonathan.

To, amma tun bayan darewarsa kan karagar mulki har ya kammala shekara hudun farko, ba a samu wanyewar matsalar tsaro a kasar ba, inda har yanzu ba ta kawo karshe ba.

Kodayake za a iya cewa, rikicin Boko Haram ya ja da baya sosai, domin kungiyar ta rage kai hare-hare wasu jihohi da kuma kwace wasu kananan hukumomi da ta yi a yankin Arewa maso Gabas, amma sababbin matsalolin tsaro sun bayyana, kamar na yin garkuwa da mutane a na amsar fansa da kuma ta’azzarar kashe-kashen Fulani makiyaya da ya watsu cikin sassa daban-daban.

Jihohi kamar jihar Kano sun samu sa’ida daga hare-haren Boko Haram tun bayan hawan Shugaba Buhari, amma jihohi irinsu Zamfara, Binuwe, Filato da Kaduna sun fuskanci kalubalen tsaron da ba su taba ganin irinsa ba tun da a ka kirkire su.

Bugu da kari, wasu daga cikin mukarraban shugaban kasar a 2015 sun raba hannun riga da shi, kamar shi Sanata Shehu Sani, tsohon gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, Sanata Dino Melaye, Gwamnan Jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da makamantansu.

A na danganta raba-garin da su ka yi da fadar shugaban kasa ba za ta rasa nasaba da rashin sauraron su da kuma yin aiki da shawarwarinsu ba. Don haka waccan magana da Sanata Sani ya yi ga Janar IBB mai ritaya a na kallon ta a matsayin hannunka mai sanda a gare shi kan yadda salon mulkin Shugaba Buhari ya ke na yin kunnen uwar shegu ga sauraron irinsu.

To, amma a al’adar dattawan Najeriya irin su IBB (idan ka zare tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Aremu Obasanjo) ba su cika fito wa bainar jama’a su na yin suka ga gwamnati ba koda kuwa sun hango kuskurenta. Yawancinsu sun fi bin wasu hanyoyi, idan su na son su nusar da ita wani abu da su ke ganin ya dace ta gyara.

To, koma dai mene ne, bangaren gwamnati da mukarrabanta lallai har yanzu su na ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen dakilewa da jigata kungiyar Boko Haram, su ke ganin inda jami’an tsaron kasar su ka takure ta waje guda.

Exit mobile version