Tsaro: Yadda Al’ummomi Suka Soma Tunkarar Masu Garkuwa

Daga Jamil Gulma,

’Yan bindiga, musamman masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, sun dade suna cin karensu ba babbaka a sassan Nijeriya, inda har ta kai ga a wadansu lokuta an ce sukan share sa’o’i da dama cikin garuruwa ko kuma kan hanya suna tattara mutane sa’ilin nan su iza keyarsu zuwa sansanoninsu, inda za su ajiye su su rika kiran ’yan uwansu suna shaida musu cewa, ‘dan uwanku yana hannu’ kuma ba za a sako shi ba sai an kawo kudi, yayin da su kuma ’yan uwa za su shiga tattalin hada kudin, domin su fanshi ’yan uwansu.

Sau da yawa wadansu sukan yi sa’a su tsere ko dai ta sanadin wadanda aka bari gadinsu sun yi bacci ko kuma wadansu hanyoyi na daban. Wadansu kuma sukan rasu ko dai ta hanyar a harbe su sanadiyyar rashin kawo kudin ko kuma saboda bakin ciki bisa ga irin wulakancin da ake yi musu a sansanin, yayin da wadansu kuma sukan fita lafiya kalau bayan an kawo kudin fansarsu.

Wannan halin ya sanya mutane yin dari-dari a duk lokacin da tafiya ta kama su, musamman a irin hanyoyin da suka hada jihohin Neja da Kaduna zuwa Abuja, Sakwkwato da Zamfara zuwa Katsina da Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja, wadanda a nan ne abin ya fi kamari a Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Sau da yawa wadannan ’yan bindiga sukan shiga gari cikin dare su kwashe sama da sa’o’i uku suna bajekolinsu ba wani mutum da zai iya daga yatsa sai dai wadanda suka sami sa’a su ranta a na kare zuwa jeji. Wadansu kuma su buya a wurare daban-daban, don ceton rayuwarsu.

Babu zancen kiran jami’an tsaro ba ne, saboda su ma ba su tsira ba, don ba su iya gaba da gaba da ’yan bindigar sanadiyyar rashin kayan aiki ingantattu da kuma irin yawansu, inda wadansu majiyoyin LEADERSHIP A YAU sun labarta cewa, wani lokacin ’yan bindigar sukan shiga gari as babura sama da 50 kuma kowane babur yana dauke da mutane biyu ko uku, sannan kuma suna dauke da bindigogi da sauran manyan makamai.

Sai dai kuma, tun kafin maganar Ministan Tsaron Nijeriya, Alhaji Bashir Salihi Magashi, ya fito karara kwanan nan ya shaida wa ’yan Nijerya su kare kawunansu, tuni wadansu al’ummomu suka dade da daukar wannan matakin, wanda sau da yawa ’yan bindiga ko mahara kan kai hari wadansu garuruwa, amma sai a yi ba-ta-kashi, inda har wani lokacin akan sami nasarar kashewa tare da kama wadansu daga cikin maharan da kuma kwace babura da makamai.

Da ya ke dai Wakilin LEADERSHIP A YAU ya tattauna da wadansu mutane da dama da ba su so a ambaci sunayensu da garuruwansu ba, saboda dalilan tsaro, a yankunan Kebbi, Sokoto da Zamfara, sun bayyana masa da cewa, yanzu sun samu saukin kai hare-hare a garuruwansu a sanadiyyar daukar matakan kare kawunansu duk da ba su bayyana matakan ba, amma dai wadansu daga cikin matakan sun hada da tanadin bindigogi da sauran makamai da kuma bai wa matasa kwarin gwiwa kan duk wani mutum ko wani yanayi da suka gani kuma ba su yarda da shi ba, to su gaya wa kwamitin tsaro da aka kafa, don daukar matakin gaggawa.

A wadansu garuruwa dake Jihar Sakwkwato yanzu haka an dauki tsawon lokaci ba a kai hari ba a cikin garuruwan da a baya mahara suka mayar saniyar tatsa a sanadiyyar daukar matakan kare kawunansu da dukiyoyinsu, kamar yadda wani matashi ya bayyana.

Ya cigaba da cewa, kwanan baya ma sun fatattaki mahara, inda har suka sami nasarar kama wadansu kuma suka kashe wadansu da dama.

Haka zalika, a satin da ya gabata a jihar Kebbi an kashe wadansu mutane biyu a garin Sauwa da ke karamar hukumar mulki ta Argungu ta hanyar kona daya, shi kuma dayan aka daddatsa shi, saboda ana tuhumar sun kashe wani mutum tare da kwace babur dinsa, inda bayan an kashe su kuma kowa ya watse, sai daga baya aka kira ’yan sanda.

Haka kuma kuma an kashe wadansu mutane hudu da aka kama da bindiga kirar AK-47 da harsasai masu yawa a garin Kende dake karamar hukumar mulki ta Bagudo da ake tuhumar masu garkuwa da mutane ne inda aka daddatsa sassan jikinsu.

Kamar yadda wadansu mutane ke kallon sojoji a matsayin sun kasa, ba haka ba ne, domin wannan yakin ya soma ne tun shekaru 30 zuwa 40 da suka gabata kuma wannan yakin ya kai ko’ina har a kauyuka, saboda akwai siyasa, addini da kuma kabilanci da kuma tattalin arziki. Saboda haka sai kowa ya bayar da tasa gudunmawa ko da za a iya shawo kan wannan matsalar ta tsaro da ta dabaibaye kasar da ke rikida daga nau’in fashi da makami, Boko Haram zuwa masu garkuwa da mutane da kuma kai farmaki a cikin garuruwa da wawashe dukiya.

Wani masani harkar tsaro Manjo Abdullahi Dankawu (Murabus) ya bayyana wa Wakilin LEADERSHIP A YAU ta wayar tarho da cewa, ba ana nufin al’umma su tunkari ’yan bindiga ko su yi fito na fito da su ba, saboda suna da miyagun makamai masu karfin gaske. Saboda haka abinda ya fi shi ne tsari na matasan ’yan banga ne ya kamata a fito da shi, wadanda su ne za su saka ido a wurare daban-daban da za a iya kiyayewa da bakuwar fuska da dai sauran alamomin da a ke tuhumar baki ne ko kuma bata-gari, a tanadar musu da makamai tare da ba su wani horo na musamman, wanda idan aka yi haka an jefi tsuntsu biyu da dutse daya. Na farko an inganta tsaro; na biyu kuma an samar da aikin yi ga matasan.

Wani basaraken gargajiya da ya zanta da wakilinmu, duk da ya ke shi ma ya nemi a sakaya sunansa bisa ga dalilan tsaro, kira ya yi ga al’umma da su kula da masu shige da fice ta ko’ina tun kama daga direbobi, ’yan acaba, cikin kasuwanni, matasa a cikin unguwanni da sauran wuraren taron jama’a da suka hada da wuraren sayen abinci da man fetur da kayan masarufi, saboda kowace irin sana’a mutum ya ke yi ya san mutanen da ya ke hulda da su a yau da gobe, saboda haka da zarar ya ga bakuwar fuska zai iya shaida ta.

Exit mobile version