Connect with us

SIYASA

Tsige Uba Nana: Masu Kwangilar Ruguza APC A Bauchi Ne Suka Fara Aikinsu, Cewar Magoya Baya

Published

on

Hadakar magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Bauchi ‘Coalition of Bauchi State APC Supporters’ sun yi tir da batun tsige shugaban jam’iyyar APC Uba Ahmad Nana da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka sanar da yi.

Inda kungiyar ta shaida cewar an dauki hayar wasu tsirarun mambobin jam’iyyar ne domin kawo rudani da tashin-tashina a cikin jam’iyyar, suna cewa babu wata madogora ta doka da masu ikirarin tube Uba Nanan ke da shi ko suka dogara da shi.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da kungiyar ta fitar dauke da sanya hannun sakataren tsare-tsare, Joseph Samuel Ciroma, ta shaida cewar sun nuna damuwarsu a bisa neman kawo rudani da wasu ke neman yi a cikin jam’iyyar.

A cewar sanarwar ta Joseph Samuel: “Hankulanmu sun karkata kan wani taron manema labaru da wani Mr Ibrahim Ago ya shirya tare da cewa sun dakatar da Uba Ahmad Nana a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi,”

Sanarwar ta zargi wadanda suka fito suka dakatar da Uba Nanan a matsayin wadanda aka dauki hayarsu domin bata wa APC da mambobinta kima, “Kwata-kwata abun da suka yi bai da wani gurbi a kundun dokoki da ka’idoji, don haka sokiburutsu ne muraran. Kuma wannan aiki ne da aka dauki nauyin wasu bata gari don aiwatarwa ba don APC suka yi ta ba sam.”

Kungiyar tana mai cewa idan ma zargin Uba Nana ake da wani kuskure ba wannan ne matakin da doka ta tanadar a bi domin ladabtar da shi ba; “Baya ga wannan ma, kundun tsarin jam’iyyar APC article 21 sub A,B,C da kuma D sun yi bayani gwara-gwara kuma filla-filla kan matakan ladabtar da dukkanin wani zababbe a wani ofis idan har akwai wani kuskure ko laifi da ya tabka,”

“A bisa wannan madogara; wadanda suka yi gaban kansu suka je suka kira taron manema labaru basu da wata madogara ta aiwatar da hakan. Shugaban jam’iyyar APC na jihar zababben shugaba ne da aka bi dukkanin matakan yin zabe da jam’iyyar ta ware a ranar 20 ga watan Yunin 2018 kuma Allah ya bashi nasarar zama shugaba,” A cewar magoya bayan APC a jihar.

Daga bisani hadakar kungiyar ta zargi gwamnatin jihar da ke ci ta PDP da daukar nauyin masu neman wargaza jam’iyyar APC a matakin jihar.

Kungiyar ta sha alwashin cewar masu neman tarwatsa jam’iyar ba za su taba kaiwa ga nasara ba, “Muna nanata goyon bayanmu da biyayyarmu wa shugabancin Uba Ahmad Nana a matsayin shugaban APC na jihar Bauchi da sauran mukarrabansa,” A cewar kungiyar.

Kan zargin da kungiyar ta yi wa gwamnati mai ci na daukar nauyin kunna wa jam’iyyar adawar wutar rikicin cikin gida, wakilinmu yayi kokarin jin ta bakin jami’an watsa labaru na jam’iyyar PDP a jihar Alhaji Yayanuwa Zainabari hakan ya citura yaki amsa wayar da muka amsa har zuwa aiko da wannan rahoton.

Advertisement

labarai