An Tsinci Gawar Wani Manomi A Dakinsa A Abuja

A cikin satin da ya gabata ne, wani makwabbacin ya shedawa wakilin mu cewar an ga gawar wani mai suna Ali dake kauyen Kubwa a cikin Birnin Tarayyar Abuja, a dakinsa wanda ya saba fita da duku-duku zuwa gona, bayan sun gaisa da safe da makwabtansa, ba’a kara ganin Ali ba a

ranar, inda saida aka balla kofar ta manomin aka kuma same gawarsa a cikin daki a cikin jin.

Wakilin mu ya gano cewar, akwai wata hatsaniya data auku a tsakanin gungun wasu matasa dake yankin kwana daya kafin aukuwar lanarin, inda hakan ya janyo aka lalata wasu wuraren da ake gudanar da kasuwanci, har wasu mutane uku da ba’a san kosu wanene ba suka samu raunuka.

Wani shugaban matasa dake yankin mai suna Daniel Christopher, wanda dan uwa ne ga marigayin, ya yi zargin cewar dan uwansa marigayin watakilan hatsaniyar ce ta rutsa dashi.

Wakilin mu ya ruwaito cewar, an bizni marigayin a ranar Juma’ar data wuce.

Duk iya kokarin da wakililinmu ya yi don jin ta bakin DPO na gundumar ta Kubwa, (CSP) Ayobami Surajudeen, akan maganar hakan yaci tura domin ance ya yi tafiya a lokacin da wakilin mu yaje ofishin kuma an kira DPO a wayar tafi da gidan ka, amma layinsa baya tafiya.

Sai dai, wani babban jami’in ‘yan sanda a ofishin na ‘yan sanda, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace an kawo rahoton maganar a ofishin na gundumar ‘yan sanda, inda ‘yan sanda suka amince aka dauko gawar marigayin daga babban asibitin dake Kubwa bayan shugabannin dake

yankin suka gabatar da bukatar a basu gawar.

Exit mobile version