Muhammad Maitela" />

Tsofaffin Kwamishinonin Shettima 4 Sun Lashe Zaben Majalisar Wakilai A Borno

Tsofaffin kwamishinonin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima tare da shugaban SEMA, sun yi nasarar lashe zabukan kujerun majalisar wakilai ta tarayya, a yankunan daban-daban da ke fadin jihar, biyo bayan sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) dangane da zabukan ranar Asabar da ta gabata.
Mutanen wadanda suka kunshi tsofaffin kwamishinoni hudu tare da shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno ( SEMA).
Tsuffin kwamishinonin, su ne na ma’aikatar kiwon lafiya, Dakta Haruna Mshelia, da takwaran sa na ma’aikatar ilimi mai zurfi, Ahmadu Usman Jaha, ta ma’aikatar albarkatun ruwa- Dakta Zainab Gimba; hadi da na kananan hukumomi da masarautu Usman Zannah, tare da Injiniya Ahmed Satomi, na hukumar SEMA, a karkashin jam’iyyar APC.
Kamar yadda hukumar INEC ta sanar, Engr. Satomi Ahmed wanda ya yi takarar a karkashin jam’iyyar APC; wanda zai wakilci al’ummar yankin Jere a zauren majalisar ya samu rinjaye ne da yawan kuri’u 82, 370 wanda ya kayar da abokin takarar sa, a jam’iyyar PDP, Bukar Shuwa mai kuri’ 8, 911.
Yayin da shi kuma Dakta Mshelia ya yi takara a mazabar kananan hukumomin Askira-Uba/Hawul a majalisar wakilan inda ya doke abokin hamayyar sa na jam’iyyar PDP da yawan kuri’u 51,763, wanda shi kuma ya samu kuri’u 30,560; tare da ba shi tazarar kuri’u 21,203.
Bugu da kari kuma, sai mace mai kamar maza; Dakta Zainab wadda hukumar INEC ta bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaben- mace tilo da ta yi nasarar shiga takara a fadin jihar Borno a jam’iyyar APC.
Dakta Zainab za ta wakilci al’ummar kananan hukumomin Bama, Ngala, Kala-Balge a majalisar wakilai ta tarayya. Kuma ta yi nasarar doke abokiyar takarar ta da yawan kuri’u 73,837, inda abokiyar hamayyar ta- Fatima Zara Saleh ta jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 6,228.
Har wala yau kuma, sai shi kuma Hon. Usman Zanah wanda ya lashe zaben a takarar kujerar; domin wakiltar jama’ar kananan hukumomin Kaga, Magumeri, da Gubio a majalisar wakilan, inda ya yiwa abokin hamayyar sa zarra da yawan kuri’u 30,683 fiye da na dan takarar PDP, Bilal Ali mai kuri’u 7,722.
A hannu guda kuma, hukumar zabe mai zaman kanta, ta ayyana Alhaji Ahmadu Usman Jaha a matsayin wanda ya samu nasarar kasancewa zabin al’ummar kananan hukumomin Chibok, Damboa, da Gwoza a zauren majalisar wakilan, da yawan kuri’u 151,031, bayan da ya tsere kishiyar sa a zawarcin kujerar- Zanna Mohammed Abbagana, na PDP mai kuri’u 21,351.

Exit mobile version