Connect with us

WASANNI

Tsofaffin ‘Yan Wasan Afrika Sun Shiga Yaki Da Korona

Published

on

Tsofaffin fitattun ‘yan wasan kwallon kafar Afirka sun shiga gasa a kafofin sada zumanta ta Intanet, a kokarin da suke na wayar da kan jama’a game da yadda za a taimaka a hana yaduwar cutar Korona a wannan yanki.

Tsofaffin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na kasa da kasa da suka hada da Ahmed Hassan na kasar Masar da Joseph Yobo na Nijeriya da Karim Haggui na Tunisiya da kuma Lomana LuaLua na Congo sun shiga cikin wannan shirin.

‘Yan wasan suna nadan faya-fayan bidiyon daban-daban inda suke kira ga al’umma yadda za’a gujewa kamuwa da annobar Korona, a wani bangare na Kamfen din  Afrika ta kasance cikin lafiya.

Yanzu haka dai cutar Korona ta haddasa rasa rayukan mutane sama da dubu 5 a Nahiyar Afirka cikin sama da dubu 200 da aka tabbatar suna dauke da ita sai dai duk da haka ana samun masu warkewa sama da wadanda suke kamuwa da ita.

Mataimakin sakatare-janar na hukumar kwallon kafar Afirka, Anthony Baffoe ya ce kwallon kafa na hada mutane da yawa dake da asali daban-daban da kabila ko yare, don haka suke fatan wannan shiri ta kafafofin sada zumunta yanar gizo, ya hada mutane wuri guda, tare da yaki da wannan annoba.

Shima mataimakin koiyan tawagar Super Eagles ta Nigeriya Joseph Yobo ya bayyana ewa wannan tsarin da suka dauka zai taimaka wajen ganin sun kawo karshen wannan annoba ta hanyar rage kamuwa da ita
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: