A ranan lahadi,10 ga watan janairun 2021 ne a karon farko a tarihin makarantar, tsofafin daliban makarantar sakandire ta karamar hukumar Lokoja ( Lokoja Local Gobernment Secondary School) aji na 2009, suka gudanar da taro a harabar makarantar dake garin Lokoja.
Taron wanda yayi armashi matuka gaya ,ya samu halartan wasu daga cikin tsofafin daliban makarantar maza da mata.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron, shugaban daliban makarantar aji na 2009, Mallam Muhammed Abdullahi wanda Mallam Muhammed Idris ya wakilta, ya bayyana farin cikinsa ganin yadda tsofafin daliban suka sake haduwa bayan shekaru goma sha biyu da kammala karatu a Makarantar,inda yace taron shine karon farko da wasu daliban makarantar suka gudanar tun lokacin da aka kafa makarantar ta LGSS,Lokoja a 1992.
Mall Abdullahi yace babban abin alfahari ne a ce dalibai yan aji na 2009 ne suka fara kiran taro a karon farko a tarihin makarantar, sannan ya godewa dukkan tsofafin daliban da suka samu damar halartan taron wadda ya bayyana shi da cewa zai kara dankon zumunci, hadin kai da kuma taimakon juna a tsakanin tsofafin daliban wadanda a yanzu suke baje a sassa daban daban na Najeriya inda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
Kazalika ya kuma yabawa wadanda suka assasa kiran taron karon farko,wato Yunusa Muhammed, Salisu Lawal, Muhammed Idris ,Amina Isiaka da kuma Sa’adat Muazu,bugu da kari da kuma wadanda suka taimaka da kwabo da dari wajen ganin an samu nasarar gudanar da taron.
Ya kuma ce a nan gaba zasu nada daya daga cikin tsofafin daliban makarantar a matsayin wanda zai kasance uban kungiyar( Life Patron) na dindindin.
Sauran tsofafin daliban da suka yi jawabi duk sun nuna jin dadinsu ganin yadda a karon farko suka sake haduwa, inda suka yi fata da kuma addu’ar ganin hakan ya dore.
A karshen taron dai, an gudanar da addu’a ga wasu daga cikin tsofafin daliban wadanda suka riga mu gidan gaskiya da kuma fatan ganin kungiyar ta dore har abada.