Khalid Idris Doya" />

Tsohon Alkalin Alkalai, Mamman Nasir Ya Rasu

Allah ya yi rasuwa wa tsohon Alkalin Alkalan Nijeriya, Maishari’a Mamman Nasir. Marigayin dai ya rasu ne da tsakar ranar jiya Asabar, bayan wata ‘yar gajeruwar rashin lafiyar da ta kwantar da shi a asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina wato ‘Federal Medical Center, Katsina’.
Marigayin dai ya rasu yana da shekaru casa’in 90 cif a duniya, gabanin jiya yana rike da Sarautar gargaji ta Galadiman Katsina, kuma, Hakimin kasar Malumfashi.
Da yake tabbatar da rasuwar, Sakataren masarautar Katsina, Bello Ifo, ya bayyana cewa, an yi jana’izar marigayin ne da karfe 4:30 na yammacin jiya Asabar a fadar marigayin da ke Malumfashi.
Gabanin rasuwar marigayin, shi ne Hakimin Malumfashi. Wakilinmu ya shaida mana cewa, dandazon jama’a ne suka hallarci jana’izar marigayin, inda tururuwar jama’a suka yi ta addu’ar Allah ya gafarta masa ya sanya aljanna ta zama makomarsa, kana dandazon jama’a ne suka nuna alhenin rashinsa.
Marigayin dai gogaggen Lauya ne kuma masanin shari’a wanda ya taka matakai daban-daban a sashin shari’a, yana daga cikin Alkalan da suka samu lambobin yabo ta kwazo da sanin aiki, ya kuma kafa tarihi sosai a rayuwarsa wanda ya zama abun alfahari ga jihar Katsina.
LEADERSHIP Ayau, LAHADI, ta nakalto tarihin rayuwar Mai shari’a Mamman Nasir da cewar an haifesa ne a shekaar 1929 a garin Katsina da ke arewacin Nijeriya.

Ya halarci kwalejin Kaduna domin samun shaidar ilimin sakandari a shekarar 1947, daga bisani kuma ya halarci jami’ar Ibadan domin samun shaidar digiri a sashin Latin.
Daga nan, ya tafi zuwa makarantar horar da Lauyoyi domin samun digiri a sashin shari’a a shekarar 1956, a wannan shekarar ce aka fara kiransa da suna Lauya ‘BAR’ a wata kotu da ke kasar Ingila a Lincoln’s Inn.
Alhaji Nasir ya dawo gida Nijeriya a wannan shekarar inda ana nadasa a matsayin Lauya mai shigar da kararraki.
A shekarar 1961 ne kuma aka nadasa a matsayin Minsitan shari’a a yankin arewacin Nijeriya, ya rike wannan kujerar na tsawon shekara biyar daga nan ya zama Daraktan a ofishin Lauyoyi masu shigar da kara a yankin Arewacin kasar nan a shekarar 1967, a wannan shekarar kuma aka sake nadasa a matsayin babban Lauya a ma’aikatar shari’a a jihar Arewa ta tsakiya a wancan lokaci.
Ya rike wannan kujerar na tsawon shekaru hudu daga nan aka sake nada shi Alkali a kotun Koli ta Nijeriya a shekarar alif 1975.
A shekarar 1978 ne kuma aka nadasa a matsayin shugaban kotun daukaka kara a Nijeriya, ya kasance a wannan kujerar har zuwa ranar da zai yi ritaya ya kammala aikin gwamnati a shekarar 1992.
Ya zama mai rike da sarautar Galadiman Katsina, an kuma yi bikin nadasa kan wannan sarautar ne a ranar 9 ga watan Mayun 1992.
Allah dai ya amshi ran, marigayin ne a ranar Asabar jiya kenan 13 ga watan Afrilun 2019 a gadon jinya a sakamakon rashin lafiyar da ta riske shi.
Wakilinmu ya nakalto cewar wannan rasuwar ya taba zukatan jama’a da daman gaske musamman al’umman Katsina, inda aka shaideshi da rike gaskiya da son jama’a, kana mai kwatanta adalci a hdimar rayuwarsa. Allah ya jikansa.

Exit mobile version