Ahmed Muhammad Dan Asabe">

Tsohon Dan Majalisar Lokoja, Hon Hashim, Ya Kwanta Dama

A ranan Asabar 30 ga watan janairun 2021 ne,Allah yayi wa tsohon dan majalisar dokokin jihar Kogi, Honorabul Hashimu Alhassan Rimi rasuwa a gidansa dake Yaragi a garin Lokoja.

Marigayin wanda ya taba wakiltar mazabar Lokoja ta Daya a majalisar dokokin jihar Kogi a zamanin mulkin jaam’iyyar PDP, ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.
Hon Hashimu Rimi gogaggen dan siyasa ne wanda yasha gwagwarmaya da kuma fadi tashi a harkar siyasa a jihar Kogi dama Najeriya baki daya.
Jama’a daga ciki da kuma wajen jihar Kogi ne ke ta aiko da sakon ta’aziyyarsu ga iyalan tsohon dan majalisar dokokin na jihar game da rasuwarsa.
Tuni dai aka yi jana’izar marigayi Hashimu Alhassan Rimi a ranan Asabar din a makabartan Unguwar Kura dake Lokoja kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Exit mobile version