Connect with us

WASANNI

Tsohon Dan Wasan Liverpool Robinson Ya Mutu  

Published

on

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool da tawagar kwallon kafar Jamhuriyar Ireland, Michael Robinson ya mutu yana da shekara 61 bayan ya shafe shekara da shekaru yana jinya.

Robinson wanda daya ne daga cikin fitattu da suka yi suna a kasar Sipaniya a harkar gabatar da shirye-shirye a kafar yada labarai ya kamu da cutar daji a shekara ta 2018 kuma tun daga wannan lokacin yake fama da rashin lafiya.

Dan kwallon yana cikin wadanda suka lashe kofin gasar Ingila a lokacin na rukunin farko da European Cup da kuma League Cup a kakarsa ta farko a Liberpool a 1983-84 sannan yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka fara kai kasar Jamhuriyar Ireland gasar cin kofin nahiyar turai.

Dan wasan ya kuma buga wasa a kungiyoyin Manchester City da Brighton da kuma Kueens Park Rangers daga baya ya koma kungiyar kwallon kafa ta Osasuna ta kasar Spaniya inda ya karkare wasanninsa a can a shekarar 1989.

Robinson ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Jamhuriyar Ireland wasanni 24 ya kuma ci kwallo hudu sannan kuma ya taba zama kaftin din tawagar a shekarun baya a lokacin da yake buga kwallon.

Tuni kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta sanar da skon ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da kuma hukumar kwallon kafa ta kasar jamhiriyar Ireland sannan kungiyoyin KPR da Brighton Albion suma sun tura sakon ta’aziyyarsu
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: