Tsohon Daraktan DSS Ga Buhari: Ka Shammaci Shugabanin Tsaro Ka Canja Su

DSS

Daga Khalid Idris Doya,

Tsohon Daraktan hukumar farin kaya (DSS) Mista Mike Ejiofor, ya bukaci Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, da ya faranta wa ‘yan Nijeriya rai ta hanyar canza Shugabanin hukumomin tsaro.

Mike Ejiofor wanda ke wannan kiran yayin da yake magana da kafar talabijin ta Channels a ranar Litinin, ya na mai cewa sauya shugabannin hukumomin tsaron zai bada damar samar da dabarun da hikimomi, samar da wadattun kayan yaki da za su kai ga samar da yanayin da za a dakile matsalolin tsaro a fadin kasar nan.

“Ina tsammanin shugaban kasa zai baiwa al’umma Nijeriya mamaki, kawai ya canza shugabanin hukumomin tsaron,” tsohon Daraktan DSS din ya nemi ‘yan Nijeriya da su sauya dabi’un su kan hukumomin tsaro

Ya ce, tare da sauke su din, za a samu dabaru, kayan aiki, sabbin shugabanin tsaro da su ma za su baje nasu fasahar da hikimomi wajen ganin an samu nasarar dakile matsalolin tsaro da suke akwai.

Tsohon Daraktan DSS din ya lura kan cewa tabbas ta hanyar sauke shugabanin tsaron za a samu nasara matuka gaya wajen rage kaifin matsalolin tsaro da suke jibge a fadin kasar nan.

A baya dai Kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya misalta kiranye-kiranyen neman a kori shugabanin tsaro da cewa abu ne wanda ba mai yiyuwa ba.

Garba ya nemi masu kiran a sauke shugabanin tsaron da su daina, yana mai cewa Buhari ne kadai ke da ikon canza su a lokacin da ya so.

 

Exit mobile version