Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja
An ja kunnen ’yan ƙabilar Ibo da kada su bari sojojin Nijeriya su riƙa yiwa ’ya’yansu rigakafin cututtuka. Tsohon gwamnan jihar Anambara, Dr Chukwuemeka Ezeife, ne ya yi wannann kira kwanan nan yayin da ya ke mayar da martani kan fargabar da a ke ganin sojojin sun haifar a jihar, ya na mai zargin cewa, za su iya yin amfani da sirinjin allura su halaka su.
Ya ƙara cewa, sanarwar da bakin duniya ya bayar bai kai ya hana su ƙin amincewa da sojojin ba. Ya ce, “a makon jiya Ina Anambara sai wani basarake ya kira ni ya shaida min cewa, an nemi mutanensa da su fito a ranar Laraba domin sojoji su duba lafiyarsu. Sai na ce ma sa a’a, manufar ita ce, idan ba mun hana su kashe su da bindiga, to ba za mu bari su kashe su da sirinji ba.”
Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya an samu taƙaddama a jihar ta Anambara kan jagoran masu rajin neman ɓallewa su kafa ƙasar Biyafara, Nnamdi Kanu, inda sojoji su na kai farmaki cikin jihar.