Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano, ya rasu a Landan yana da shekaru 70 bayan doguwar jinya.
Majiya daga iyalinsa ta ce ya sha fama da matsalar zuciya da kuma matsalolin da suka shafi cutar sankarar mafitsara.
Wani ɗan uwansa ya ce ya sha fama da rashin lafiya kafin rasuwarsa.
ADVERTISEMENT
Majiyar ta ce likitoci sun ajiye shi a dakin kula da marasa lafiya ta musamman (ICU).
Mutuwarsa na zuwa ne makonni kafin ya bayyana a kotu a Nijeriya.
An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar.
Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022.













