Daga Abubakar Abba,
Tsohon Gwamnan jihar a karkashin inuwar jamiyyarsa ta APC Zamfara, Abdulazeez Abubakar Yari, ya karyata rahoton da wasu kafafen yada labarai suka wallafa na cewa kotu ta bayar da umarnin a kwace dala miliyan 621 daga gunsa.
Tsohon Gwamnan jihar ya karyata rahotannin ne ta hanyar wani wakilinsa mai suna Abdulrahman Yahaya a cikin wata sanarwa day a fitar ya kuma rabarwa da manema labarai, inda Tsohon Gwamnan jihar Abdulazeez Abubakar Yari, ya yi Allah wadai da rahotannin da wasu kafafen yada labaran suka wallafa.
A cewar Abdulrahman Yahaya, asalin abinda ya faru shi ne, kotun ta bayar da umarnin da a rufe asusun ajiya na bankin da Tsohon Gwamnan jihar Abdulazeez Abubakar Yari yake ajiya wato asusun bankunan Polaris da kuma na Zenith, inda ya ajiye naira miliyan 278.
Wakilinsa na tsohon gwamnan Abdulrahman Yahaya ya kuma yi kira ga ‘yan jarida dasu tabbatar da sun tantance sahihancin rahotannin su kafin su wallafa domin a kaucewa aukuwar matsala.