Daya daga cikin tsofaffin ‘yan wasan babbar tawagar kwallon kafar Najeriya, Joe Erico ya mutu yana da shekaru 72 kamar yadda iyalansa suka shaidawa hukumar wasanni ta kasa a ranar Juma’ar
Mai tsaron raga Erico na daga cikin masu horar da babbar tawagar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles a gasar cin kofin nahiyar Afrika ta shekarar 2000 da aka yi a Lagos, kuma ya taimaka wa Najeriya ta samu tikitin shiga gasar Afcon da na kofin duniya a shekarar 2002.
Tsohon kocin wanda masoyansa ke wa lakabi da ‘Jogo Bonito’ wato wani salon wasa da aka san Brazil da shi na tattaba kwallo, ya rasu ne a Lagos bayan gajeriyar rashin lafiyar da ake dangantawa da cutar Korona.
A safiyar Alhamis ne jami’in yada labaran tawagar Super Eagles, Babafemi Raji ya tabbatar da rasuwar tsohon mai tsaron ragar inda kuma ya mika sakon ta’aziyya ga iyalansa da kuma daukacin ‘yan Nigeriya masoya kwallon kafa.