Daga Hussaini Yero
Mataimakin Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakala Liman ya canza sheka daga jam’iyyarsa ta APC zuwa PDP.
Wakala ya sanar da ficewa daga APC ne a yau Laraba a Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara.
Tsohon mataimakin gwamnan ya kwashe tsawon shekaru 8 a matsayin mataimakin Gwamna Abdul’aziz Yari a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
“Ganin yadda gwamnatin jam’iyyar PDP ta ke taka rawar gani wajen ci gaban jihar ta kowane sashe, kuma gwamna Bello Muhammad Matawallen Maradun yana amsar shawarwarina domin ci gaban jihar, shi ne ya kara min kwarin gwiwar canza sheka zuwa ga Jam’iyyar PDP.” inji Malam Wakala.