Tsohon Minista, Mahmud Tukur Ya Rasu

Tsohon Ministan kasuwanci da masana’antu, a zamanin mulkin soja na Janar Buhari, Dakta Mahmud Tukur, ya mutu da cikin daren Juma’a, 9 ga watan Afrilu, 2021 a birnin tarayya Abuja.

Mahmud Tukur ya taba zama shugaban Jami’ar Bayero, Kano.

Majiyoyin sun bayyana cewa ya mutu ne bayan an garzaya da shi asibiti a Abuja daga gidansa dake Kaduna a daren jiya Alhamis.

Exit mobile version