Tsohon Ministan Wasanni Ya Canza Sheka Zuwa APC A Kebbi

Jami’iyyar APC reshin jihar kebbi ta kaddamar da bukin karbar tsohon Ministan Wasanni a lokacin shugaban kasa Olusegun Obasanjo, wato Dakta Samaila Saidu Balarabe Sambawa kan Canza sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar ta kebbi tare da magoya bayansa.

An gudanar da bukin taron na karbar tsohon Ministan Wasanni da kuma jama’arsa a filin taron Malakar gwamnatin jihar kebbi da ke a Haliru Audu a Birnin-kebbi.

A jawabinsa na maraba shugaban jam’iyyar APC ta jihar kebbi Barista Attahiru Maccido yace “jihar kebbi tana daya daga cikin jahohin da ke kare martabar APC da kuma jawo mutanen jam’iyyar adawa ta PDP zuwa ga jami’iyyar mai mulki kasar nan a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari” . Hakazalika ya ci gaba da cewa APC jihar ta kebbi na kan samun nasarori a jihar a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu na ganin cewa ta tatar watsa jami’iyyar adawa  watau PDP a jihar ta kebbi da kuma kasar nan bakin daya.

Daga karshe ya yi murnar ga ganin wannan rana ta tsohon Ministan Wasanni da jama’arsa sun dawo jam’iyyar APC a jihar kebbi, ya kuma godewa tsohon Ministan da kuma jama’arsa da duk jama’ar da suka halarci bukin taron.

Shi ma da ya ke gabatar da jawabinsa watau tsohon Ministan Wasanni a tsayawar gwamnatin Obasanjo, Dakta Samaila Saidu Balarabe Sambawa ya bayyana cewa “ mun shigo jam’iyyar APC jihar mu ta kebbi  ne saboda irin ayyukkan Alhairi da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Gwamna Abubakar Atiku Bagudu keyi a kasar nan”. Ya ci gaba da cewa “ babu wani alkawari da aka yi damu ko magoya bayan mu domin shiga jam’iyyar APC a jihar ta kebbi”.   Bugu da kari ya shugaban kasa Muhammadu Buhari na alfahari da jihar kebbi kan irin abubuwan da Gwamna Bagudu ke yiwa jihar kebbi da kuma Nijeriya bakin daya.

Daga nan ya godewa shuwagabanin Jami’iyyar APC ta jihar kebbi da kuma gwamnatin jihar kan irin Karama wa da aka yiwa sa da kuma da jama’arsa.

A jawabinsa na rufe bukin taron Sanata Abubakar Atiku. Bagudu Gwamnan jihar ta kebbi ya bayyana Jindadinsa da kuma godiyarsa ga mutanen da suka ga yadace su dawo a cikin jam’iyyar APC domin irin ci gaban da take samarwa ga jama’ar jihar kebbi da kuma Nijeriya baki daya.

Daga karshe ya yi hori jama’ar jihar kebbi da su cigaba da wanzarda Zaman lafiya a jihar kebbi da kasar mu Nijeriya.

 

Exit mobile version