A Cote D’iboire jam’iyyar PDCI mai kawance da jam’iyyar Shugaban kasar RDR, ta bakin shugaban ta tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie, na sa ran a samu sauyi ta fuskar shugabancin kasar Cote d’Iboire.
Bedie ya bayyana haka ne gaban duban magoya bayan jam’iyyar tareda cewa a lokacin zaben 2011, sun cimma matsaya ta cewa a shekara ta 2020,jam’iyya mai ci a yanzu za ta mika ragama zuwa jam’iyyar da ta mara masu a zaben da ya gabata, sabili da haka magoya bayan shugaban kasar su daina kawo rudani ga salon tafiyar siyasar gungun jam’iyyoyi da suka dafawa Shugaban kasar Ouattara.
Medico: Girgizar Kasa Ta Hallaka Sama Da Mutane 200
Girgizar kasa mai karfin gaske da ta aukawa tsakiyar kasar Medico, tayi sanadin mutuwar sama da mutane 200, tare da rusa daruruwan gidaje.
Girgizar kasar mai karfin maki 7.1 da ta jijjiga makwabtan ihohin Medico City, ta auku ne jim kadan bayan daruruwan ‘yan kasar ta Medico, sun kammala karbar horon ceto da kuma bada agajin gaggawa a duk lokacin da aka samu girgizar kasa.
Ko a farkon watan Satumba, sai da wata girgizar kasar mai karfin maki 8.1 da ta aukawa kudancin kasar ta hallaka mutane 90.