A Cote D’iboire jam’iyyar PDCI mai kawance da jam’iyyar Shugaban kasar RDR, ta bakin shugaban ta tsohon Shugaban kasar Henri Konan Bedie, na sa ran a samu sauyi ta fuskar shugabancin kasar Cote d’Iboire.
Bedie ya bayyana haka ne gaban duban magoya bayan jam’iyyar tareda cewa a lokacin zaben 2011, sun cimma matsaya ta cewa a shekara ta 2020,jam’iyya mai ci a yanzu za ta mika ragama zuwa jam’iyyar da ta mara masu a zaben da ya gabata, sabili da haka magoya bayan shugaban kasar su daina kawo rudani ga salon tafiyar siyasar gungun jam’iyyoyi da suka dafawa Shugaban kasar Ouattara.