Shafin intanet na jaridar DAILY SABAH da ke kasar Turkiyya ya bayar da rahoton cewa wata tsohuwa Ba’amurkiya mai shekara 60 a duniya ta yi shahada ta karbi Musulunci sakamakon dabi’un sufancin da ta gani a fim din Ertuğrul da aka yi a kan tarihin Daular Usmaniyya.
Shafin ya ruwaito cewa matar wadda aka sa wa suna Khadija da ke zaune a birnin Wisconsin na Amurka ta fada wa Kamfanin Dillancin Labaru na Anadolu Agency (AA) cewa dabi’un Shehun da ya rika tarbiyyantar da Ertuğrul (babban jarumin fim din), Ibnil Arabi ya zaukantar da ita ta musulunta.

Ta kara da cewa a gabadayan fim din babban gwaninta shi ne Ibnil Arabi, “a wasu lokutan kalamansa sukan sa ni zub da hawaye. A gaskiya ba ni da gwani kamarsa a fim din. Fim din ya yi matukar birge ni ta yadda ya ja ni na kalli zangonsa guda hudu duka, na kara maimaitawa har sau hudu. Na sha tsayar da kallon (abin da wasu ke ce wa “danna sitof”) idan na ci karo da wani abu da ban gane ba, sai na nemi karin bayani a shafin intanet. Da haka na fara neman karin bayani kan abin da Musulunci ya kunsa da kuma tarihin Daular Usmaniyya” In ji ta.
Kamar yadda Khadija ta nunar, yadda Ibnil Arabi yake bayani a game da Allah (SWT) da Musulunci da zaman lafiya da adalci da yadda ake taimakon wadanda aka zalunta a cikin fim din ya girgizata.
Khadija wacce a baya Kirista ce mai bin Cocin Baptist ta ce kyawawan dabi’un da jaruman fim din suka rika nunawa sun karya mata zuciya. Ta kara da cewa “kallon fim din ya warware mun mishkiloli da dama game da Addinin Musulunci.”
Daga nan ne ta fara karanta Alkur’ani mai fassara da Turanci, daga bisani kuma ta musulunta a wani Masallaci mafi kusa da ita.
A wani bayani da ta yi da ya nuna imaninta da kuma tarbiyyar da ta samu daga Ibnil Arabi a fim din, Khadija ta ce, “Ina godiya ga Allah a kullu yaumin. Ina gode masa saboda sabuwar rayuwar da ya ba ni. Mutane ba su fahimci cewa rayuwar nan takaitacciya ba ce. Sakona ga mutane shi ne kar su tsaya bata lokutansu wajen aikata abubuwan tir. Rayuwa ba ta ta’allaka ce ga irin suturar da kake sawa ba, ko irin motar da kake hawa. Ka yi tafakkuri da kyau.” In ji ta.
Sharhi:
Alhamdu Lillah. Idan har wani Sufi a fim zai iya karya zuciyar wacce ba musulma ba ta musulunta, to ina ga Sufin da ya yi ido biyu da mutum? Ballantana ma a ce Sufin nan SHEHU IBRAHIM INYASS (RTA) ne MAGAJIN SHEHU TIJJANI shugaban masu darikun sufaye kaf? Shi ya sa babu mamaki tarihi (kamar yadda Turawan Ingila duk da kin su da Musulunci suka rubuta a gidan tarihinsu) ya bayyana cewa SHEHU IBRAHIM ya musuluntar da sama da mutum dubu hudu (4,000) a Ghana, a rana daya kuma lokaci guda. Su kuwa mutanen kasar da abin ya faru suka ce mutum dubu 10,000. Shi kuma Shehun da ya yi abin, ya ce dubban mutane ne ba adadi.