Daga Khalid Idris Doya
Hatsarin mota ya ci rayuwar tsohowar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi Dakta Zuwaira Hassan Ibrahim da sanyin safiyar yau Litinin.
Zuwaira ta zama kwamishinan lafiya a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar, Muhammad Abdullahi Abubakar, ta rasu ne sakamakon wani hatsarin mota da ya rutsa da ita a daidai kauyen Zaranda da ke da nisan kilomita 36 kacal da cikin garin Bauchi.
Dakta Zuwaira ta rasu ta na da shekaru 46 a duniya, ta kuma kasance gabanin rasuwarta it ace shugaban sashin Community Medicine, College of Medicine, da ke asibitin ATBUTH.
Dan uwan mamaciyar, Alhaji Adamu Garkuwa wanda jami’in watsa labarai ne na hukumar Nigeria Security and Civil Defence Corps (NDCDC) reshen jihar Bauchi ya tabbatar da mutuwar nata, ya na mai cewa za a sallaceta ne da karfe daya na Litinin din nan gami da bisneta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Ya shaida cewar ta rasu ne a daidai kauyen Zaranda a hanyarta na dawowa daga Jos ta jihar Filato, ya nuna kaduwarsu a bisa rashin ‘yar uwan tasu, ya na mai nunata a matsayin hazika, jarumar da take kokari a bangaren aikinta tare da hidimta wa al’umma.