Khalid Idris Doya">

Tsohuwar Minista, Okonjo-Iweala, Ta Zama Shugabar Cibiyar Kasuwanci Ta Duniya

Masaniyar tattalin arziki kuma tsohuwar ministar kudin Nijeriya, Ngozi Okonjo-Iweala ta zama mace ta farko kuma ‘yar Afrika ta farko da za ta shugabancin hukumar kasuwanci ta Duniya (WTO), bayan tabbatar da nadinta a ranar Litinin yayin wani babban taron masu ruwa da tsaki kan tattalin arzikin Duniya suka gudanar.

Kafin dai tabbatar mata da wannan kujerar, Okonjo-Iweala ta sha suka daga wasu bangarori inda daga baya ta samu nasarar dalewa kan wannan kujerar, duk da cewa hukumomi a Nijeriya sun bada tasu gudunmawar wajen dafa mata har zuwa lokacin da ta samu nasarar kaiwa ga wannan kujerar da ta jima tana nema.

Tunin dai hukumomi da wasu manyan ‘yan Nijeriya suka fara nuna murnarsu da kasancewar mace ta farko kuma ‘yar asalin kasar da ta samu nasarar zuwa ga wannan babban mataki a duniyance, lamarin da ke kara bayyana musu farin cikinsu da fatan cewa Nijeriya na da damar shiga harkokin daban-daban domin a dama da su a duniyance.

Daga cikin kalubalen da ta fuskanta har da kakkausar suka musamman daga gwamnatin Amurka da ta gabata karkashin Donald Trump wanda ta ki amincewa da goya mata baya duk da kasancewarta mai rike da shaidar zama ‘yar kasar.

Wannan dai ne karon farko a tarihin hukumar da mace kuma daga Afrika za ta jagorance ta bayan karewar wa’adin Roberto Azebedo da ya jagoranci hukumar.

A shekarar 2019 ne Ngozi ta samu shaidar zama ‘yar kasar Amurka bayan shafe shekaru 25 a harkokin tafiyar da bankin na duniya kana shekaru 8 matsayin ministar kudin Nijeriya.

Bayanai sun nuna an haifi Ngozi ranar 13 ga watan Yunin 1954 a garin Ogwashi-Ukwu na jihar Delta, mahifinta Chukwuka Okonjo Farfesa ne tun a wancan lokaci da ya fito daga gidan sarautar Ogwashi.

Ngozi Okonjo-Iweala ta fara karatun Firamare a Kueens School da ke Enugu kana St. Anne da International school a Ibadan gabanin tafiya jami’ar Habard da ke Amurka a 1973 inda ta karanta tsimi da tanadi kana ta samu digirin-digirgir a fannin tattalin arziki kana ta ci gaba da karatu a jami’ar Massachusetts inda tan karanta fannin hada-hada kana kasuwancin zamani a jami’ar.

Ngozi Okonjo-Iweala wanda yanzu ke da shekaru 66 a duniya ta yi aure ta na kuma da yara 4 mace guda maza 3.

Yanzu haka dai Ngozi ta kafa tarihin zama bakar fata kuma mace ta farko da ta hau wannan kujera ta shugabancin hukumar kasuwanci ta Duniya, inda aikinta zai fara daga ranar 1 ga watan Maris mai zuwa.

Exit mobile version