Tsokaci Kan Hanyoyin Tallafa Wa Gwamnati A Kokarinta Na Samar Da Zaman Lafiya

Zaman Lafiya

Mai karatu barkanmu da sake saduwa a wani karo na wannan fili namu, inda muke ankarar da junanmu, musamman matasanmu game da abubuwa ko hanyoyin da za a bi wajen ci gaban al’umma a harkokin yau da kullum, wanda kuma wannan abu yana kunshe ne a hanyoyi da dama, ta yadda kowa da irin gudumawar da zai bayar a cimma nasarar abin.

Ga duk mai bibiyar wannan shafi namu zai lura da cewa mun fi mayar da hakali ne wajen wasu muhimman abubuwa guda biyu, wadanda suka hada da harkar ci gaban matasa da kuma harkar samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Tabbas ko ba a fada ba, wadannan abubuwa guda biyu su ne ginshikan ci gaban kowace al’umma daga kowace nahiya, musamman bisa la’akari da cewa matasa ne suka fi yawa a cikin al’umma, kuma su ne ake amfani da su wajen samar da rashin zaman lafiya. Don haka za mu iya cewa abubuwan nan guda biyu tamkar abu daya ne.

Saboda haka ko a yau ma maudu’in namu yana nan a wannan dabaka ne, domin yana da muhimmanci mutum ya kasance yana ankare da duk wani abin da zai kasance na tashin hankali ne, mutumin nan kuwa matashi ne ko dattijo. Za a iya gane haka ta hanyar mu’amalar mutum da jama’ar da yake cudanya da ita.

Ko da wane lokaci yana da muhimmanci mutum ya zama yana duba abubuwan da za su kawo ci gaban al’umma, musamman ta fannin samar da zaman lafiya da fahimtar juna, mutum ya ga cewa wace gudumawa yake bayarwa don samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummarsa da yake zaune a ciki.

Kada ke nan ya kasance ya zama wanda a kullum shi ba shi da wani aiki sai haddasa fitina, ko kuma neman hada wani da wani, ko kuma mutum ya ware kansa ya rinka yin abubuwa shi kadai, wato tamkar yana kyamar jama’ar da yake zaune a ciki.

A watannin baya na taba yin wani rubutu a wannan shafi game da batun nan na yadda wasu kan saki bakinsu wajen furta duk abin da ya fito, ba tare da tunanin matsalar da zai iya haifarwa ba, mutum ya saki ya jefa magana mai zafi, wacce ya san za ta bata wa abokin zaman sa rai.

Lallai ko shakka babu, kowane mutum da Allah ya yi, ya yi shi da irin nasa tunanin, kowa da yadda yake kallon abu idan ya zo masa, kamar yadda yake kuma kowa da irin nasa ra’ayin. Wasu ana iya kawar da su daga kan ra’ayinsu mummuna ko kyakkyawa, wasu kuma ba yadda za a yi a iya kawar da su daga ra’ayin da suka ginu a kai.

Irin wannan ra’ayi da fahimta da Allah ya yi wa kowa tasa daban, shi ne ya kamata a ce kowa ya tsaya a kan nasa, kada wani ya ce dole sai kowa ya bar nasa ya dawo nasa. Idan kowa ya rike nasa, to ba yadda za a a ce an samu wata hatsaniya game da fahimtar wani. Kamar yadda karin maganar Hausawa ke cewa ‘DUNIYA ZAMAN DAN MARINA, KOWA DA INDA YA SA GABANSA!’

A irin wannan yanayi ne ya zama sai ka taras da wani ko wasu suna furta kalaman da za su kawo rudani, wani lokaci ma har yakan kai ga jawo tashin hankali a tsakanin jama’a. Duk irin wadannan abubuwa, ba wani abu ke jawo su ba illa rashin girmama addini, fahimta, kabila ko martabar wani, wanda hakan kuma ke zama babbar barazana ga zaman lafiyar al’umma. Domin wajibi ne, muddun ana tare, to a girmama juna.

Kalaman batanci, ba abin da suke jawowa illa rarraba da tashin hankali a tsakanin jama’a. Wasu lokulata ma, abin takaici za ka taras da irin wadannan kalaman suna fitowa ne daga bakin shugabannin addini, wadanda suka hada da Malamai da Fastoci, wanda maimakon su zama masu hada kan al’umma, sai ya zama sun zama masu rabawa, ta yadda za ka ga wasu shugabannin addinin sun bar koyarwar addinin nasu sun koma suna bin ra’ayin kansu, kuma da haka suke jan magoya bayana.

Haka kuma ko ma a cikin addinin, mutum zai taras da cewa ya-su ya-su ma suna cusa irin wannan kiyayya ta hanyar furta kalaman bantanci da cusa kiyayya ga mabiyansu na sauran al’ummar da suke da bambancin fahimta ko ra’ayi da su, inda a wasu lokuta abin har ya kan kai ga zubar da jini. Abin bakin cikin ma wasu lokuta za ka taras da ’yan gida daya ne, amma ba a ga-maciji da juna.

Baya ga addini, wani bangare kuma da ake amfani da irin wadannan kalamai na cusa kiyayya a tsakanin al’umma, shi ne bangaren siyasa, wanda za a iya cewa kamar abin ya fi muni ta nan. Domin za ka ga dan siyasa ya dage yana ta furta kalamai na batanci, wanda zai cusa mummanar kiyayya idan abokin hamayyarsa ya ji, wanda ta haka sai ya a ginu a cikin kiyayya da gaba.

Baya ga fannonin addini da siyasa, hatta a tsakanin jama’a ma akwai lokutan da wasu jama’a za su rinka furta irin wadannan kalamai na cusa kiyayya da batanci, wasu lokuta kawai don su haddasa gaba da kiyayya, ko kuma don cimma wata manufa tasu ta kashin kansu. Ta yadda za ka ga wasu lokuta ko a cikin hira ma sai kawai ka ji mutum ya soka wa dan uwansa wata magana, wanda in ba hankali aka yi ba, nan da nan sai a tashi da tsiya.

Duk idan muka bi wadannan fannoni na addini, siyasa da zamantakewa, za mu ga cewa babu bukatar a rinka tofa, ko furta irin wadannan kalamai. Domin a har kullum babu wani abu da suke haifarwa, kamar yadda na fada a sama, illa gaba da kiyayya, wasu lokuta ma har ta kai ga zubar da jini, wanda idan da an bi abin da ya dace, to hakan ba za ta faru ba.

Sannan KALAMAN CUSA KIYAYYA, wadannan a bayyane suke, wato kalamai ne da mutane kan yi don kawai su jawo kiyayya da tsana a tsakanin jama’a. Da irin wannan wasu ke ganin cewa wai idan an hana su furta wasu kalamai, ko an kama su don sun yi haka, sai su rinka ganin tamkar an tauye masu hakki ne fadin albarkacin baki, musamman a tsarin mulki irin na dimokradiyya.

Saboda haka yana da muhimmanci kowa ya san yadda zai rinka tafiyar da harkokinsa na zamantakewa a tsakanin jama’a, kowa ya san mene ne idan ya furta zai zama ya bata ma abokin zamansa rai, mene ne kuma zai yi wanda zai zama ya samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Wannan shi ne abin da ya wajaba kowa ya mayar da hankali a kai. Muna fata Allah ya shige mana gaba ya yi mana jagoranci a duk harkokinmu nay au da kullum.

Exit mobile version