Connect with us

RAHOTANNI

Tsokacin Jakadun Kasashen Nijeriya Da Nijer Da Ghana Kan Taron Kolin FOCAC Na 2018 A Beijing

Published

on

A gabannin taron koli na dandalin tattaunawar hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka ko kuma FOCAC a takaice, wanda aka kaddamar da shi a rainakun 3 da 4 na watan Satumban 2018 a birnin Beijing, jakadun kasashen Najeriya, Nijer da kuma Ghana, sun yi tsokaci game alfanu da moriyar dake tattare da wannan muhimmin taro musamman wajen kyautata dangantaka dake tsakanin Sin da Afrika da kuma irin moriyar da taron zai kawowa al’ummonin bangarorin biyu.

Wakilin sashin Hausa na gidan radiyon kasar Sin CRI Ahmad Inuwa Fagam ya zanta da jakadun kasashen uku bi da bi, inda suka bayyana yadda suke hangi makomar taron dandalin wanda Sin ta karbi bakuncinsa a wannan karo.

Jakada Baba Ahmad Jidda na Najeriya dake kasar Sin ya fara da tofa albarkacin bakinsa game da taron kolin na FOCAC inda ya ce taron zai kara samar da moriya ga jama’ar Sin da kasashen Afirka, inda ya bayyana muhimmanci da alfanun dake tattare da taron kolin, ya kuma nuna yabo ga manufar gwamnatin kasar Sin na karfafa zumunci da kasashen waje, musamman kasashen Afirka da kuma shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya’. Ya ce bayan taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU, babu wani taro dake hada shugabannin Afrika a waje guda don su samu damar tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban kasashensu sama da taron FOCAC. Ya ce taron yana baiwa shugabannin kasashen Afrika damar tattaunawa kai tsaye da shugaban kasar Sin Xi Jinping game da batutuwan da suka shafi yin hadin gwiwar tattalin arziki da zuba jari da kulla yarjejeniyoyi kan samar da muhimman kayayyakin more rayuwa da ci gaban al’ummomin kasashen biyu. Jakadan ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci taron tare da wata babbar tawagar jami’an gwamnati da manyan ’yan kasuwa da masu zuba jari. Ambasada Jidda ya ce, baya ga batun tawagar da ta kunshi masu zuba jari da manyan ’yan kasuwar da suka taho daga Najeriyar, akwai kuma tattaunawar da za’a gudanar tsakanin jami’an kasashen Najeriyar da na Sin. Jakadan na Najeriya ya ce, kasarsa tana daukar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da muhimmanci wadda suka shafe sama da shekaru 47 da kulla dangantakar tsakanin Sin da Najeriyar. Najeriya tana farin ciki da manufofin diplomasiyyar kasar Sin musamman irin yadda Sin take mu’amala ta gaskiya da Najeriya ba tare da tsoma baki ko yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar ba. Ya ce kasar Sin tana ci gaba da kyautata mu’amalarta ba ma da kasashen Afrika kawai ba, har ma da sauran kasashen duniya bisa kyakkyawar fahimtar juna da take da shi misali game da hadin gwiwar Sin da kungiyar BRICS, da kuma shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya” wanda kasar Sin ce ta bullo da ita, wadda ta ratsa hanyar siliki ta kan teku, da kuma hade sauran nahiyoyin duniya a karkashin shawarar ta “ziri daya da hanya daya”.

Shi ma a nasa tsokacin jakadan kasar Ghana a kasar Sin Ambassada Edward Boateng, ya bayyana dangantakar dake tsakanin Ghana da Sin a matsayin dangantaka mafi daraja kuma mai dadadden tarihi, a matsayinta na kasar da ta kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Sin tun a shekarar 1960, kuma ta bude ofishin jakadancinta a kasar Sin. Jakadan na Ghana ya ce, dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin ta samo asali ne tun zamanin shugaban kasar Ghana na farko Osagyefo Kwame Nkrumah, a zamanin shugabancin jagoran jamhuriyar jama’ar kasar Sin na wancan lokaci Mao Zedong. Ambassada Boateng ya ce, akwai kyakkyawan hadin gwiwa mai karfi ta fuskar ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Game da batun taron dandalin hadin kan Sin da Afrika kuwa wanda kasar Sin za ta karbi bakuncinsa a watan Satumbar shekarar nan ta 2018, jakadan ya ce, tun bayan kafa dandalin na FOCAC shekaru 18 da suka gabata, ya zuwa yanzu, an samu nasarori masu yawan gaske tsakanin bangarorin biyu, wanda a cewarsa hadin gwiwar ta baiwa kasashen Afrika damammaki masu yawa wajen samun ci gaba musamman ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa da yaki da fatara da kuma sana’o’in dogaro da kai da dai sauransu. Sannan ya yi amana cewa kasar Ghana a shirye take ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen cin moriyar juna musamman a bangaren samar da hanyoyin layin dogo, tinunan mota, gine ginen gidaje da dai sauransu. Ya ce a shekarar 1972 kasar Ghana ta jefa kuri’ar amincewa da kasar Sin ta zama wakiliyar din din din a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya, ya ce a lokacin da marigayi Kofi Annan ya zama babban sakataren majalisar dinkin duniya wanda dan asalin kasar Ghana ne, ya yi kokari matuka wajen zurfafa dangantaka tsakanin MDDr da kasar Sin. A zamanin shugaban kasar Ghana John Kuffor ya kafa wani tsarin hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasarsa da kasar Sin, tun a wancan lokacin, Ghana ta gudanar da wani muhimmin aiki na farko mafi girma a kasar wanda wani kamfanin samar da lantarki na kasar Sin ya gudanar da shi a kasar ta Ghana, sannan akwai wasu muhimman ayyukan raya kasa da kasar Sin ta gudanar a Afrika wanda kasar Ghana tana sahun gaba wajen amfana da ayyukan. Ya ce dangantaka tsakanin kasar Ghana da kasar Sin ba sabon abu ba ne, abin da kawai ake bukata shi ne daukar sabbin matakai na kara kyautata alakar dake tsakanin kasashen biyu wanda kuma shi ne abin da Ghana ta sanya a gabanta a halin yanzu. Jakada Boateng ya ce dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wani muhimmin ginshiki ne na yin mu’amala da cudanya tsakanin gamayyar kasashe kuma mu’amala ce ta kasa da kasa, sannan wata babbar dama ce ta samar da bunkasuwar ci gaba ta fuskar samar da hasken lantarki da gina muhimman kayayyakin more rayuwa a kasashen Afrika wadanda su ne jigo wajen magance fatara da samar da guraben ayyukan yi wanda zai kyautata rayuwar al’ummomi mazauna nahiyar kuma babbar dama ce da dandalin FOCAC ya bullo da shi. A halin yanzu, dandalin FOCAC ya cika shekaru 18 da kafuwa kuma hakika ya kasance wani tsari ne da za’a iya cewa ya kafu da kafafunsa a halin yanzu. Ya ce taron wanda kafatanin shugabannin kasashen nahiyar Afrika za su halarce shi kuma za su gana da babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, domin su tattauna game da inda aka kwana da irin nasarorin da aka cimma karkashin inuwar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika da kuma duba bangarorin da ya kamata a ba da fifiko don kyautata mu’amalar dake tsakanin bangarorin biyu da kuma amfanawa al’ummomin kasashe Sin da na Afrika. Ya ce kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba ne ta hanyar mutunta al’adunta, da martaba hakkin jama’arta, da kuma amincewa da manufofin kasarta, wannan shi ne abin da Afrika muke bukatar koya daga kasar Sin. Ya ce alal misali “idan kasashen Afrika na bukatar taimako daga kasashen yammacin duniya ana gindaya musu wasu sharruda masu yawa amma a karakshin dandalin FOCAC babu wasu sharruda da ake gindayawa, wannan yana daga cikin abin da ya fi burge ni game da wannan hadin gwiwar,” in ji Boateng. Jakadan na Ghana ya ce karkashin yarjejeniyoyin da aka cimma a taron Johannesburg wanda gwamnatin Sin ta alkwarta ware kudi kimanin dala biliyan 60 don aiwatar da muhimman ayyuka karkashin inuwar dandalin FOCAC, ya ce ana fata a taron FOCAC na wannan Beijing na watan Satumbar 2018, za’a kara samar da karin kudade domin cike gibin ayyukan samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afrika musamman a fannonin ci gaba ilmi, kiwon lafiya, layin dogo, ruwan sha, fannin ma’adanai da bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika. Ambasada Boateng ya ce ya kamata kasashen Afrika su koyi wasu muhimman darrusa daga kasar Sin kamar sadaukar da kai da jazurcewa, kishin kasa, dabi’ar hangen nisa, yin da’a, da dabi’ar nan ta yin aiki tukuru, domin ci gaban al’ummomin nahiyar Afrika. A nasa bangaren jakadan jamhuriyar Nijer a kasar Sin ambasada Inoussa Mustapha ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin kasar Sin da Afrika hulda ce da ta shafe shekaru aru-aru, hulda ce wadda kasashen Sin da Afrika suke cin moriyar juna da cudanya tare a matsayin “Ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda” wannan ne ma tasa mahukuntan kasar Sin karkashin shugabancin jagoran jamhuriyar jama’ar kasar Sin shugaba Xi Jinping bisa hangen nesan da ya yi, a shekarar 2000 ya yi tunanin kafa dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika wato FOCAC a takaice, don kyautata mu’amala, da cudanya, a tsakanin bangarorin biyu. Ya ce kasar Sin ta daura damara wajen tallafawa Afrika a kokarin da kasashen ke yi na bunkasa ci gaba tattalin arzikinsu da ci gaban zaman rayuwar al’ummomin nahiyar. Ya ce taron FOCAC na Beijing na 2018, ya kasance tamkar wata ’yar manuniya ce dake tabbatar da irin nasarorin da aka cimma cikin shekaru ukun da suka gabata tun bayan taron kolin FOCAC na baya bayan nan da aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu a shekarar 2015, inda kasashen Afrika suka ci gajiya a fannonin gina kayayyakin more rayuwa, aikin gona, yaki da fatara, samar da guraben ayyukan yi, da bunkasar tattalin arzikin kasashen na Afrika.  (Ahmad Inuwa Fagam, ma’aikacin sashen Hausa na CRI)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: