Bayan wancan gwamna da ke son zama shugaban Kasa, ya sake samun damar zarcewa zangon mulki na biyu, sai wani sabani ya shiga tsakaninsa da waccan kungiyar matasa da yake bai wa makamai, saboda haka, nan take, sai ya sake kirkirar wata sabuwar kungiya ta matasa ful, wadda za ta yi masa maganin waccan kungiyar ta farko, su ma sai ya tsiri ba su makamai.
Ba tare da bata wani lokaci ba, sai wadancan mabanbantan kungiyoyi biyu da duka gwamna ne ya kage su, su ka antaya cikin farmakar juna da manya-manyan makaman da gwamna ne ya saya musu, duka dai, a kan hanyarsa ta cimma burinsa na siyasa.
Sai a ka wayigari, guda daga cikin wadancan kungiyoyi biyu, gwamnatin tarayya na mara mata baya, dayar kuwa (“yar borar), wadda ta samu sabani da maigirma gwamna, sai a ka gurfanar da shugabansu a Kotu, a na ma tuhumarsa. Wannan yanayi ne ya bayu zuwa ga tasowar wadancan kungiyoyi biyu (na gwamna), zuwa ga gwabza fada a tsakaninsu, a karshe ma dai kacokan suka narke zuwa ga kungiyoyin yan-ta'adda. Su ka yi gayar karfi, ga su da makamai fal a hannu. Su fasa bututu, su saci danyen mai son ransu. Wai ma daga karshe, sai aka canja musu suna da alkibla zuwa ga kungiyoyin
yan fafutuka, wadanda ke gwagwarmayar samowa yankinsu hakkunansu na tattalin arziki, da kuma son a yi wa yankin nasu adalci.
“Kai Simon”! Tsaya ka ji, in ji tsohon kwamishinan `yan sanda;
“… Zan iya nuna maka sunayen wasu rikakkun yan ta'adda da ke a Kudanci da Arewacin wannan Kasa, wadanda su ka wahalar da jami'an tsaro na
yan sanda ainun, za ka ga akasarin yan ta'addar, da za a bi diddigi, sai a samu cewa,
yan siyasar da, kodai, ke neman mulki, ko kuma, masu son tabbata bisa karagun mulki, su ne su ka samar da irin wadancan kungiyoyin matasan `yan ta’adda”.
Dan-jarida Simon Kolawale ya cigaba da cewa, kaf a Najeriya, babu wata jiha da a yau za a kalla a ce, yan siyasarsu ba su da irin nasu nau'in
yan ta’addarsu da su ke dankawa makamai a ranakun ZABE!. Hana rantsuwa, sai dai a cikin birnin tarayyar wannan Kasa, wato Abuja, a nan ne kadai ba a kirkiri ko samar da yan dabar siyasa, ko kuma jagororinsu a garin ba. Dalilin rashin kyankyashe
yan dabar siyasa a Abujan kuwa, a fili ne yake karara. Amsa, saboda babu GWAMNA a birnin na Abuja. Sai dai MINISTA. Shi ko mukamin minista a birnin, nadi ne, ba zabe ne ake yi a kai ga hawa matsayin ba. Shugaban Kasa ne ke da alhakin nada shi.
Da a yau a Abuja, za a yi tunanin samar da kujerar gwamna a garin, babu shakka, yan siyasar da za su nemi kujerar, nan da nan ne za a ga sun fara samar da
yan jagaliya dauke da makamai a garin. Daga nan ne kuma, ita ma Abujar za ta yi sallama da zaman lafiya. Dan-jarida Kolawale, ya cigaba da zayyana batutuwan da su ka tattauna da wancan tsohon kwamishinan `yan sandan kamar haka;
“…Ya fada min asalin abinda ya samar da Matasan kungiyar Ekomog (sunan yan dabar siyasa a Borno), wadanda bayan kammala Zaben Shekarar 2003, akasarinsu su ka shiga kungiyar
yan ta’addar Boko Haram. Bugu da kari, ya (tsohon kwamishinan yan sanda) yi min karin haske game da Matasan
yandaba (matasan da ke rike da makamai dare da rana) na Kano, wadanda a lokutan zabe a ke amfani da su a matsayin `yan ta’addar siyasa…”.
Simon Kolawale ya cigaba da fadin cewa, tsohon kwamishinan, ya fada min jagororin irin wadancan kungiyoyi na yan ta'addar siyasa, wadanda ke da irin nasu sansani a Kudu-maso-Yammacin wannan Kasa. Wadanda suma su ka jima da yin kaurin-suna cikin aikata nau'i-nau'i na ayyukan ta'addanci, irinsu kashe-kashen mutane na ba gaira ba dan-dalili, tare da aikata ta'adar garkuwa da mutane. Kuma duk irin wadannan ayyuka na ta'addanci da za a ga su na yi, babu wani hukunci da ke biyo baya, saboda da irin manya-manyan
yan siyasar da su ke tare da su, wadanda ke sa su aikata aika-aika a nahiyar. Wasunsu, zancen nan da ake yi, tuni sun jima ne da rasuwa. Sannan, da mutum kuma zai dubi jihar Benue, zai ga akwai wani kasurgumin dan-ta’adda, wanda za a iya kwatantashi da marigayi Terwase Akwaza da ke a can Kasar Ghana. Babban dan-ta’addar Binuwen, za a same shi yana jagorantar kungiyoyin yan ta'adda makasa, tare da yi wa
yan siyasa aiki. Saboda haka, sai ya gawurta, ya zamto kwata-kwata ma ba ya tabuwa.
Sanarwa ta musamman:
Sakamakon wani sauyi da aka samu, muna sanar da masu karatu cewa wannan shafi naku mai farin jini zai koma jaridarmu ta ranar Talata, a matsayin Mukalar Talata. Da fatan za a biyo mu domin jin karashen wannan batu da aka fara tattaunawa a kai da kuma wadanda za su biyo baya.
Edita