Mustapha Ibrahim Abdullahi" />

Tsokar Jikin Mutum (3)

08037183735 musteeibr10@yahoo.com

Satikan da suka wuce, na danyi bayani akan tsokokin da suke a sassa daban daban a jikin mutum.

A mafi yawan bayanan da nayi, ban tabo tsokar naman dake bayan mutum ba; kuma nayi nazari na fuskanci yin bayanin su ko yaya yake, akwai karuwa a ciki.

Tsokar baya an kasa ta gida biyu: kashi na farko sune na waje, wadanda suka taso daga kahon kashin baya zuwa wuya, da hannaye. Kaso na biyu ya kunshi tsokoki da suke shimfide a gadon baya. Asalin su ya taso ne tun daga kugu har ya zuwaa tushen wuya da kai.

Wadannan tsokoki Aikin su shine daidaita tsayuwa kyam, wanda bature yake kira “posture”. Bugu da kari, suna taimaka wajen tallafawa motsawar kashin baya. Rauni ko ciwo kan shafi wadannan tsokoki a sakamakon daukar abubuwa masu nayi ta hanyar da bata dace ba.

Za ku iya gujewa yiwa wadannan tsokoki rauni ta hanyar tsugunawa yayin daukar Abu mai nauyi sosai. za’a a iya sunkuyawa a dauki abu a kasa, amma an gaano cewa; durkusawa ko tsugunawa yafi kubuta daga samun waccan matsalar

Kaso na biyu na tsokar baya wanda ya kunshi tsokokin da suke shimfide a gadon bayan an sake kasa shi gida uku: na farko akwai tsokoki na sama-sama, akwai na tsakaiya, akwai kuma na can ciki.

Wadanda suke a sama-saman guda biyu ne: Na farko, yawansu ya kai bakwai kuma sun taso ne daga kahon kashin baya (spinous processes) na wuya gua bakwai. Na biyu kuwa, sun taaso ne daga kahon kasusuwan baya na bangaren wuya guda 7, sun kare a fika-fikan kasuwan baya na bangaren wuyan dai( Kamar yadda zamu gani nan gaba, mafi yawan kasusuwan baya suna da fikafikai, kaho, jiki, da kuma tushe). A ma’ana, aikin da sukeyi shi ne kula da motsawar kasusuwan baya zuwa ga gefen hagu ko dama.

 

A na kiran su da “erector spinae”, wato masu mikar da kashin baya. Sun taaso ne daga kashin baya da yake a tsakanin kugu guda biyu da kuma kashin baya da yake wajen duwawu, sai sukayi sama domin su dafe a jiki kasusuwan hakarkari daga baya( kashin hakarkari kamar kwando yake; akwai a gaba, akwai a baaya.

Na karshe, wato na can ciki suma aiki iri daya suke yi da wadancan dda na fada. Suna taimakawa wajen mikar da kashin baya, juya shi gefe da gefe, da kuma tankwara shi yayi sunkuyo.

Idan na ce kashin baya, ba wai kashi daya nake nufi ba, a’a. Ina nufi nufin kasusuwan da suka fara tun daga bayan wuya har ya zuwa karshe. A dabbobi masu jela, kasusuwan dake jelar har zuwa kashin baya da wuya da zaku bi asalin su.

A dunkule, tsokar naman dake bayan mu, tana taaka muhimmiyar rawa wajen abubuwa da daama kamar zama, tafiya, daukar abu mai nauyi, kwanciya da tashi, tsugunawa, yunkuri, da sauran su.

Kuma dai wadannan tsokoki na baya suna tabbatar da kasusuwan hakarkari a mazaunin su, da hana su gocewa, da kuma tallafa musu wajen daidaito bisa tsari mai kyau.

Shin ko kunsan akwai tsoka guda shida da suke kula da jujjuyawar iadnun mu? Akwai mai rike idanu daga sama domin kar su sako-sako suyo kasa ko suyi gefe, Akwai mai tokare ido daga kasa domin kar ya dinga yin can sama ko yayi gefe.

Haka kuma ragowar guda hudun sune kamar haka: daya tana juya ido gefen hagu, daya tana juya shi gefen dama, daya tana jan ido kasa idan mutum yana so ya kalli kasa, dayar kuma tana daga ido sama idan mutum yana so ya kalli sama.

Akwai kuma tsokar da ta ke rufe idanu. Ita ma ta sama da ta kasa. Idan mun zo bayani a kan ido, zan fadada idan Mai Duka Ya so.

 

Exit mobile version