Tsoron Shan Ƙasa Ya Sa Elrufa’i Ɗage Zaɓen Jihar Kaduna —Sarkin Gandu

Daga Balarabe Abdullahi, Zariya

An bayyana babban dalilin da ya sa gwamnatin Jihar Kaduna ta umurci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar da ta sake ɗage zaɓen ƙananan hukumomi da ta ce za ta yi a ranar 30 ga watan Disambar wannan shekara ta 2017, da cewar saboda jam’iyyar gwamnati ta hango jam’iyyar PDP za ta lashe zaɓuɓɓukan da za a yi ne.

Shugaban jam’iyyar PDP na ƙaramar hukumar Zariya, kuma Sarkin Gandun Zazzau, Alhaji Sama’ila Musa Ɗan Arewa ne ya bayyana haka a yayin gabatar da tsokaci kan sake ɗage zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Kaduna da hukumar ta ce za ta yi a ranar da aka ambata.

Alhaji Sama’ila Musa ya ci gaba da cewar,tun da gwamna El-rufai ya kasance gwamnan Jihar Kaduna,babu wani ayyukan ci gaba da gwamnatin ta aiwatar, ya ce baya ga rushe wa al’umma gidajensu, da tantance ma’aikata, bashi da wata alƙibla.

Ya ci gaba da cewa, babu wani ɗan Jihar Kaduna da ya san abin da ya ke yi, da zai sake zaɓen  gwamna El-rufai, musaman idan an duba halin ƙunci da kuma taraddadin da ya sa ma’aikatan Jihar Kaduna a ciki.

Da kuma Sarkin Gandun Zazzau Alhaji Sama’ila musa ya juya ga ‘yan majalisar Jihar Kaduna, ya tunatar da su cewa akwai ranar ƙin dillanci,wato ranar da za su koma ga jama’ar da suka zaɓe su. Ya ƙara da cewa, a wannan rana ce al’ummar da suka tura su wannan majalisa za su nuna masu abin da ke cikin zukatansu.

Alhaji Sama’ila wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Zariya, ya ce ba wai magoya bayan jam’iyyar APC kawai ba, hatta ma’aikatan Jihar Kaduna na jiran ranar da za su nuna baƙin cikinsu na matsaloli daban-dababn da gwamnatin Jihar Kaduna ta tsoma su a ciki.

A ƙarshe, Alhaji Samaila Musa Ɗan arewa, ya ce, jan ƙafar da ake yi a Jihar Kaduna da ya shafi zaɗen ƙananan hukumomin jihar, ɓata lokaci ne kawai ake yi, domin gudun mugun ji da mugun gani. “Jam’iyyarmu ta PDP ta riga ta shirya, yanzu abin da muke jira kawai ranar da za a yi zaɓen.” Inji shi

Exit mobile version