Tuhumar Da Ake Min Siyasa Ce Kawai -Saraki

Sanata Saraki ya yi jinjina ga Kotun koli ta Nijeriya da ta yanke hukuncin wanke shi daga duk tuhumar da gwamnatin tarayya ta shigar gaban kotun da’ar ma’aikata, tuhume-tuhume guda 18 gwamnatin tarayya ta shigar, inda kotun da’ar ma’aikata ta wanke shi, daga bisani sai aka sake neman Sarakin da ya kare kanshi a kotun daukaka kara akan wasu tuhume-tuhumen guda uku daga cikin 18 da aka yi watsi da su.

Hukuncin da Kotun ta yanke ya yi matukar faranta min rai, wannan ya kara sa min fata a kan makomar kasar mu, sannan ya kara min fata a kan kotunan kasar mu, Sannan ina matukar mika godiya ta ga Allah wanda shine ya bani wannan nasara, ya wanke ni daga tuhume-tuhume na karya da ake yi don a bata min suna, inji Saraki

Saraki ya ce, ‘Ni mutum ne da ya yi amanna da yaki da cin hanci da rashawa, duk wanda ya san ni ya san mutum ne mai yaki da cin hanci da rashawa tun ina gwamna nake daukar matakan dakile cin hanci da rashawa.

Exit mobile version