Connect with us

KASASHEN WAJE

Tumbatsar Madatsar Ruwa Ta Hallaka Mutane 34 A Ghana

Published

on

Akalla mutane 34 ne suka hallaka a arewacin kasar Ghana, wasu biyu kuma suka bace, sakamakon ambaliyar da ta aukawa yankin, dalilin saukar ruwan sama mai karfi, da kuma tumbatsar madatsar ruwa Bagre da ke Burkina faso mai makwabtaka da kasar ta Ghana.

Madatsar ruwan na Bagre ya soma ne daga kogin Bolta da ya taso daga Burkina Faso har zuwa yankin kudancin Ghana.

Mataimakin hukumar bada agajin gaggawa na kasar Ghana Seji Seji yace zuwa yanzu, ambaliyar, ta shafi sama da mutane dubu 52,000.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: