Daga Mahdi M. Muhammad,
Karamin Minista na Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Prince Clem Agba, ya bayyana cewa, ci gaban tattalin arzikin Nijeriya ya yi matukar raguwa a cikin shekaru biyar da suka gabata.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da yake gabatar da matsakaicin tsarin ci gaban kasa (MTNDP) na shekarar 2021 zuwa 2025, a wani taron jin ra’ayoyin jama’a da kwamitin majalisar wakilai kan tsara kasa da ci gaban tattalin arziki ta gudanar.
Ya cigaba da cewa, tattalin arzikin kasar ya bunkasa da matsakaicin kasa da kashi biyu cikin dari a lokacin.
Ministan ya ce, rashin ci gaban tattalin arziki mai inganci, kasar na da mafi karancin GDP na kowane mutum duk da cewa ita ce kasar da ke kan gaba wajen samar da mai a Afirka, kuma mamba ce a kungiyar kasashe masu fitar da man Fetur (OPEC).
Agba ya ce, Nijeriya ita ce kasa mafi girma, kuma mafi yawan tattalin arziki a Afirka, tare da GDP na dala biliyan 446 da yawan jama’a kimanin miliyan 206 a shekarar 2020.
Haka zalika, Ministan ya ce, yawan kudin shigar da take samu na dala 2,156.51 a shekarar 2020, kaso 19 ne kawai na adadin duniya.
“Nijeriya, kamar sauran kasashe masu tasowa, tana fuskantar matsaloli masu daure kai wadanda za su hana ta cimma burinta na ci gaba,” in ji shi.
A cewarsa, MTNDP za ta kafa kakkarfan tushe don fadada tattalin arziki, ta hanyar bunkasar MSME da kuma yanayin kasuwancin da zai fi jurewa.
Ya ce, manyan tsare-tsaren tattalin arzikin mai na bayan Nijeriya sun hada da nazarin Ajandar 2063 na kungiyar tarayyar Afirka (AU), da kungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta 2050 da kuma cigaba (SDG) 2030.